Jami'in Kwastam da Ya Yi Fatali da Cin Hancin $50,000 Ya Samu Karin Girma
- Hukumar Kwastam a shiyya ta A ta samu sabuwar shugabanci tare da alkawarin ƙara karfafa yaki da fasa-kauri a Najeriya
- Tsohon kwamanda ACG Mohammed Salisu Shuaibu ya bayyana nasarorin da aka cimma cikin watanni bakwai na jagorancinsa
- Sabon kwamanda Gambo Iyere Aliyu ya yi alkawarin gina tsarin zamani, ladabi da kuma kokarin bin doka a rundunar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Wa'adin Shugaban hukumar kwastam na shiyya ta A a Najeriya, ACG Mohammed Salisu Shuaibu, ya zo karshe.
Ya kuma mika ragamar shugabanci ga sabon kwamandan yanki, Gambo Iyere Aliyu, wanda ya yi suna saboda matsayarsa a kan karban cin hanci.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa an gudanar da bikin mika mulkin ne a ranar 10 ga Disamba 2025, wani muhimmin lokaci a tsarin yaki da fasa-kauri na hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu saabbin shugaba a hukumar Kwastam
A cikin jawabin bankwana, ACG Shuaibu ya gode wa Allah da kuma Shugaban Kwastam na Kasa, Bashir Adewale Adeniyi, bisa amincewa da tallafi da suka ba shi damar jagorantar shiyya ta A cikin nasara.
Ya ce watanni bakwai da ya yi — tun daga 23 ga Afrilu 2025 — sun kasance cike da kalubale da samun nasarori, inda babban aikinsa shi ne ƙarfafa ayyukan leken asiri da inganta dabarun bincike.
ACG Shuaibu ya bayyana irin gagarumar nasarar da tawagarsa ta samu yayin aikinsa inda aka samu kwace haramtattun kaya da darajarsu ta kai ₦10,051,812,208.
Wadannan sun haɗa da buhuna 23,000 na shinkafar ƙetare, motoci 98, kilogiram 2,350 na tabar wiwi, jarkokin mai 1,820, bindigu 15, da alburusai 4,841.
Ya kara da cewa an samu kama jirage marasa matuka manya biyu, kilogiram 25 na haramtattun kwayoyi, da kuma tulunan bam 4 na ƙasar Rasha.
Sabon kwamandan Kwastam ya kama aiki
Da yake mayar da martani, sabon kwamanda Gambo Iyere Aliyu ya gode wa CGC da shugabancin hukumar bisa amincewa da suka yi da shi.
Ya yabawa ACG Shuaibu bisa kyakkyawan jagoranci, yana mai alƙawarin ci gaba daga inda ya tsaya domin kare mutuncin Najeriya.
Sabon Kwamandan ya ce zai martaba manufofin shugaban hukumar — wanda suka haɗa da yaki da fasa-kauri ta hanyar dabarun leken asiri, haɗin kai da masu ruwa da tsaki, da kuma inganta walwalar jami’ai.
Ya jaddada muhimmancin shiyya ta A a matsayin garkuwar tattalin arzikin ƙasa, yana mai cewa ƙwarewa, gaskiya da ladabi za su kasance ginshiƙai uku a mulkinsa.
Kwastam ta cafke mota dauke da haramtattun kaya
A baya, kun ji cewa Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Seme ta sanar da kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da muhimman sinadarai da ake amfani da su wajen hadar bam.
Jami’an hukumar sun yi nasarar cafke motar ne yayin wani samame da suka kai a lokacin sintiri da binciken kayayyakin da ake shigo da su ta iyakar kasar, tare da wallafa bidiyon binciken.
A cikin bidiyon an ga jami’an sun gane cewa lamarin ya wuce shakku, domin motar na ɗauke da abubuwa masu hadari, lamarin da ya sa aka kama motar domin zurfafa bincike a kanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


