An Shigar da Ganduje Kara wajen Tinubu, Ribadu kan Kafa Hisbah a Kano
- Kungiyar lauyoyin Kano ta nemi Bola Tinubu da NSA su dakatar da shirin kafa sabuwar Hisbah ƙarƙashin Gidauniyar Ganduje
- Lauyoyin sun ce tsarin na iya tayar da tarzoma da rikice-rikice a jihar Kano idan ba a dakatar da Abdullahi Umar Ganduje ba
- A daya bangaren kuma, Gidauniyar Ganduje ta ce shirin na da nufin samar da aikin yi da yi wa addini hidima ne ba siyasa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sabon ce-ce-ku-ce ya kunno kai a Kano bayan da kungiyar lauyoyi ‘yan asalin jihar ta zargi tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje da kokarin kawo rikici a shirin kafa Hisbah mai zaman kanta.
A korafin da ta yi, kungiyar ta ce wannan shiri na Dr. Abdullahi Umar Ganduje na iya zama barazana ga tsaron jihar da zaman lafiyar al’umma.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa kungiyar ta aika da takardar koke ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi karar Ganduje wajen Tinubu da Ribadu
A cikin takardar korafin da Usman Imam Tudun Wazirichi, PhD, da Rita Benedict, Esq. suka sanya wa hannu, kungiyar ta ce akwai yunkurin kawo tashin hankali a Kano domin cin moriyar siyasa.
Sun bayyana cewa wasu abubuwa da suka faru kwanan nan a wasu sassan jihar sun nuna akwai shiri na ƙirƙirar rashin tsaro da gangan.
Lauyoyin suka gargadi gwamnati da cewa bai kamata a kirkiri wata runduna da sunan Hisbah mai zaman kanta ba, saboda hakan zai iya zama mafaka ga mutane masu tsattsauran ra’ayi ko masu aikata laifi.
The Guardian ta rahoto cewa sun ce:
“Tsaro aikin gwamnati ne, ba na kungiyoyi ko wani bangare ba.”
Martanin Ganduje kan kafa Hisbah a Kano
Rahotanni sun nuna cewa Gidauniyar Ganduje ta fara shirin daukar mutum 12,000 a karkashin kungiyar Hisbah mai zaman kanta.
Baffa DanAgundi ya ce manufar wannan shiri ita ce samar da aikin yi ga wadanda aka sallama daga hukumar Hisbah ta jihar.

Source: Facebook
Ya ce shirin na son taimaka wa al’umma ne ta fuskar ayyukan addini, ba wai don siyasa ko haifar da sabani aka kawo shi ba.
Hujjojin da lauyoyin Kano suka kawo
Kungiyar lauyoyin ta jaddada cewa sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulki ya fayyace cewa tsaro da walwalar jama’a shi ne babban aikin gwamnati.
Saboda haka, a cewarsu, duk wani yunƙuri na kirkirar rundunar tsaro ba a karkashin dokokin gwamnati ba, zai saba wa tsarin mulki kuma ya iya haifar da rikice-rikice a Kano.
An caccaki Ganduje kan shirin kafa Hisbah
A wani labarin, kun ji cewa tsohon kwamishinan Kano, Muaz Magaji ya caccaki Abdullahi Umar Ganduje kan shirin kafa Hisbah.
Muaz Magaji ya bayyana cewa lamarin wani yunkuri ne na neman kawo babban rikici da Gandjue zai yi a karshen rayuwarsa.

Kara karanta wannan
'Hisbar Ganduje za ta jawo hallaka rayuka a Arewa,' Tsohon kwamishina ya yi gargadi
Jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyi daban-daban game da maganganun tsohon kwamishinan a kan Abdullahi Ganduje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

