Bayan Ganawar Sirri, An Ji Abin da Gwamnatin Najeriya Ta Fadawa Tawagar Amurka

Bayan Ganawar Sirri, An Ji Abin da Gwamnatin Najeriya Ta Fadawa Tawagar Amurka

  • Gwamnatin Tarayya ta gabatar wa tawagar 'yan Majalisar dokokin Amurka hakikanin abin da ke faruwa a Najeriya
  • Tawagar Amurka ta kawo ziyara Najeriya ne domin gudanar da bincike da gane wa idonsu gaskiya kan zargin kisan kiristoci a kasar
  • Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ya tabbatar da cewa sun fada wa tawagar Amurka cewa matsalar tsaron Najeriya ba ta da alaka da addini

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - A makon nan, tawaga ta musamman daga Majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin bincike kan zargin kisan kiristoci.

A wannan ziyara, tawagar ta gana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya.

Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi.
Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) Hoto: @LOFagbemi
Source: Twitter

Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ya gana da tawagar 'yan majalisar Amurka da jakadan kasar a Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Majalisa ta shiga tsakani, da yiwuwar a yafewa mutane bashin COVID 19

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake hira da manema labarai bayan ganawar sirri, Fagbemi ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba ta da alaka da addini, kuma bai kamata a danganta ta da bambancin addini ba.

Abin da Najeriya ta fadawa tawagar Amurka

Fagbemi ya ce a taron, gwamnatin tarayya ta gabatar wa tawagar Amurka ainihin matsayarta kan ayyukan ta’addanci da tashin hankali da ke addabar kasar nan.

“Mun yi masu bayanin da ya kamata tun lokacin da muka je birnin Washington, kuma ina farin cikin ganin cewa sun zo nan kasar domin su gani da idonsu.
"Muna da kalubale na tsaro, kuma gwamnati na yin iya bakin kokarinta wajen shawo kansu.”

- In ji Lateef Fagbemi.

Yadda gwamnatin Najeriya ke gurfanar da yan ta'adda

Ministan ya bayyana cewa ma’aikatarsa ke da alhakin gurfanar da wadanda ake zargi da ta’addanci, kuma duk shari’o’i na bin tsarin doka.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Zambar N5bn: Gwamnatin Tinubu ta gurfanar da tsohuwar minista a kotun Abuja

“Daga 2017 zuwa 2025, gwamnati ta samu nasarar hukunta 860, sannan an sallami wasu 891 saboda babu hujja.
"Wannan ya nuna cewa muna bin doka. Ba mu kama mutum haka kurum mu tura kurkuku, sai an yi bincike sosai, wanda ba shi da laifi a sake shi.”

Ya kara da cewa gwamnati na mutunta duk hukuncin da kotu ta yanke ko dai na kama mutum da laifi ko na wanke wanda ake zargi.

Lateef Fagbemi.
Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi tare da tawagar Amurka bayan ganawar sirri a Abuja Hoto: @LOFagbemi
Source: Facebook

Fagbemi ya gargadi jama’a da su daina sa wasa ko son zuciya wajen bayyana halin tsaron kasar nan, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

"Ina mai tabbatar muku da cewa abin bai kai munin da ake fada ba. Muna da matsaloli, amma ba matsalar addini ba ce," in ji shi.

'Yan tawagar Amurka sun ziyarci Benuwai

A wani rahoton, kun ji cewa tawagar 'yan Majalisar Amurka ta kai ziyara jihar Benuwai a wani mataki na bincike kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya tabbatar da ziyarar 'yan Majalisar Amurka a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa sun tattauna muhimman batutuwa.

Kara karanta wannan

Tawagar Amurka ta dauki jiha 1 a Arewa, ta kawo ziyara kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Daga baya tawagar ta kuma ziyarci Cocin Katolika da ke kusa da Gidan Gwamnati, inda suka sake wata ganawa ta sirri da Bishof Wilfred Anagbe na majami'ar Maki da wasu manyan limamai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262