Tinubu Ya Bada Umarni kan Kare Manyan Najeriya bayan Janye 'Yan Sanda

Tinubu Ya Bada Umarni kan Kare Manyan Najeriya bayan Janye 'Yan Sanda

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ministan Cikin gida ya tsara yadda za a bayar da kariya ta musamman bayan janye jami’an ’yan sanda
  • Za a maye gurbin ’yan sandan da aka janye da jami’an hukumar tsaron fararen hula domin kada manyan mutane su fada cikin barazana
  • Gwamnati na neman sake fasalin tsarin tsaro saboda ƙalubalen garkuwa da mutane da ta’addanci da zummar kare rayukan 'yan sanda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi aiki tare da Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa da hukumar NSCDC bayan janye yan sanda daga tsaron manyan mutane.

A cikin umarnin, Shugaban Kasan ya bayyana cewa bai kama a bar manyan mutanen a cikin haɗari bayan janye jami’an tsaro da aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Bayan korafe korafe, Tinubu ya bada sabon umarni kan janye 'yan sanda daga gadin manya

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin kare manyan Najeriya
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a ranar 23 ga Nuwamba, 2025 Shugaban ya bada umarnin a cire dukkannin ’yan sandan da ke yi wa manyan mutane rakiya a fadin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin Shugaba Bola Tinubu ga 'yan sanda

Daily Post ta wallafa cewa wannan umarni ya fito ne a lokacin wani taron tsaro da ya gudana tare da Sufeton yan sandan Najeriya, Hafsoshin sojojin ƙasa da sama, da shugaban hukumar DSS.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan mataki na nufin ƙara ƙarfafa tsaron da ’yan sanda za su ba wa jama'a a cikin al’ummomi, musamman wuraren da ba su da isassun jami’ai kuma ana fuskantar rashin tsaro.

Da yake jawabi kafin a fara zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ranar Laraba, Tinubu ya ce ministoci ko wasu jami’an gwamnati da ke buƙatar kariya saboda nauyin aikinsu su sanar da Sufeton yan sanda.

Shugaban Najeriya ya ba Nuhu Ribadu umarni
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hotpo: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya ce:

“Idan kun samu wata matsalar tsaro saboda irin aikin da kuke yi, ku tuntubi Sufeton yan sanda ku samu sahalewata.”

Kara karanta wannan

Sanata ya yi kumfar baki a majalisa bayan janye masa 'yan sanda

Shugaban ya umarci Tunji-Ojo da ya yi daidaito da IGP da NSCDC wajen maye gurbin jami’an ’yan sanda da aka janye da na Civil Defence domin kada muhimman mutane su kasance cikin fargaba ko barazana.

Gwamnati na shirin sake fasalin tsarin tsaro

Tinubu ya kuma umarci Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro (NSA) da hukumar DSS su tattara karin bayanai tare da kafa kwamitin da zai sake nazarin tsarin tsaro gaba ɗaya.

Ya jaddada cewa wajibi ne a aiwatar da wadannan matakai ba tare da jinkiri ba, domin Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale na garkuwa da mutane da ta’addanci.

A cewarsa:

“Ina sane da cewa wasu daga cikin mutanenmu yanzu suna cikin haɗari. Saboda haka dole mu samar musu da kariya ta musamman. Jami’an tsaron fararen hula suna da makamai, kuma ina so Mashawarcin Shugaban Kasa ya tabbatar da cewa ana ɗaukar batun masu gadin dazuzzuka da muhimmanci.”

Tinubu ya ce gwamnati za ta yi amfani da dukkannin rundunonin da take da su domin kare rayuka da dukiyar ‘yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa babu wani ɓangare na al’umma da za a bari a cikin barazana.

Kara karanta wannan

An ƙara yawan ƴan sanda a Adamawa don hana faɗan kabilanci

An kara yawan 'yan sanda a Adamawa

A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da cewa ta tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa Karamar Hukumar Lamurde, domin shawo kan sabon rikicin kabilanci.

Wannan mataki ya biyo bayan dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnatin jiha ta ayyana domin dakile tashin hankalin da ya barke bayan wasu mutane sun hauro yankin Lamurde daga jihar Gombe.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya roki mazauna yankin da su mutunta dokar hana fita tare da zama a cikin gidajensu domin kare rayukansu da kuma ba yan sanda jami'an.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng