Majalisa Ta Shiga tsakani, da Yiwuwar a Yafewa Mutane Bashin COVID 19

Majalisa Ta Shiga tsakani, da Yiwuwar a Yafewa Mutane Bashin COVID 19

  • Majalisar Wakilai ta shiga tsakani yayin da 'yan Najeriya da suka ci bashin COVID-19 ke ci gaba da ganin sakon cire kudi a asusun ajiyarsu
  • A zaman ranar Laraba, Majalisar tarayyar ta tattauna kan yadda za a yafe wa mutane wannan bashi duba da halin matsin da ake ciki
  • Wani 'dan majalisa daga jihar Neja, Hon. Musa Sa'idu Abdullahi ya ambaci kasashen duniya da suka yafe wa mutane irin wannan lamuni

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da duk wani cire kudi kai tsaye daga asusun wadanda suka ci gajiyar lamunin COVID-19.

Majalisar wakilai ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta yafe wa talakawa da kananan ‘yan kasuwa wannan rancen kudi da suka karba a lokacin annobar cutar COVID-19 a 2020.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure a majalisar tarayya kan batun da Ya shafi batan fiye da N16trn a CBN

Majalisar Wakilai.
Mambobin Majalisar Wakilan Tarayya yayin da suke tsakiyar zamansu a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Leadership ta ce wannan matakin ya biyo bayan kudirin gaggawa da dan majalisa daga Neja, Hon. Musa Saidu Abdullahi, ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin da aka rabawa 'yan Najeriya

Hon. Musa ya tunatar da cewa gwamnatin tarayya ta hanyar bankin CBN da NIRSAL Microfinance Bank ta kafa tsarin COVID-19 Targeted Credit Facility (TCF) a lokacin annobar.

Ya ce karkashin wannan shiri, gwamnatin Najeriya ta raba N419.42bn domin rage wa talakawa da ‘yan kasuwa radadin halin matsin da aka shiga sabola kulle.

Ya kara da cewa shirin ya taimaka wajen kafa sababbin kasuwanci ko tsare kusan ayyukan yi 1,585,872 a fadin kasar daga barazanar kora.

'Dan majalisar ya ce zuwa watan Satumba 2023 akwai Naira biliyan 261.07 (kimanin 62%) da wadanda suka ci bashin ba su biya ba.

Abin da ya hana mutane biyan bashin COVID-19

Ya ce binciken bankin CBN ya nuna cewa mutane sun gaza biyan bashin ne sakamakon hauhawar farashi sama da 24%, karancin abinci, talauci da karyewar kasuwanci.

Kara karanta wannan

'Za a iya kara fuskantar juyin mulki a Afirka ta Yamma,' Femi Falana

Hon. Musa Abdullahi ya ce:

“Lamunin COVID-19 tallafi ne na tsira, ba lamunin kasuwanci ba, yawancin mutane sun yi amfani da kudin ne wajen sayan abinci, lafiya, haya da karatun yara.”

'Dan majalisar ya ce a shirin lamunin Anchor Borrowers ma an yi sassauci wajen biyan bashin duk da yawan wadanda suka gaza biya, don haka TCF ya fi cancantar afuwa kasancewar tallafi ne na lokutan wahala.

Majalisa ta nemi a yafewa 'yan Najeriya

Majalisar ta ce kasashe kamar Amurka, Kanada, Jamus, Afrika ta Kudu da Indiya sun yi afuwa ko tsawaita wa'adin biyan lamunin COVID sabida yanayin jin-kai.

Hon. Musa Abdullahi ya yi gargadi cewa:

“Ci gaba da cire kudi kai tsaye daga asusun wadanda suka ci bashin yana lalata rayuwar talakawa, ruguza kasuwanci, yana kara rashin aikin yi, kana yana iya tayar da tarzoma.”
Nirsal Microfinance Bank
Bankin Nirsal Microfinance, wanda ya jagoranci ba da lamunin COVID-19 ga yan Najeriya Hoto: @Nirsal
Source: UGC

Ya kuma yaba wa CBN da NIRSAL saboda kafa shirin, wanda ya ce ya ceci miliyoyin iyalai daga kuncin annobar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: 'Dan Majalisar Tarayya ya burma matsala, an kore shi daga YPP

An yi rikici mai zafi a Majalisar Wakilai

A baya, kun ji cewa rikici ya barke a zaman Majalisar Wakilai lokacin da aka gabatar da kudirin da ya nemi a gayyato gwamnan CBN, Yemi Micheal Cardoso.

Hatsaniyar ta auku ne bayan gabatar da kudiri da ya nemi a gayyaci gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, domin ya yi bayani kan zargin kin tura N16.3trn zuwa baitul mali.

Rigima ta kaure tsakanin yan Majalisar ne lokacin da Hon. Ghali Mustapha Tijjani daga Kano ya gabatar da gyara a kudirin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262