Burkina Faso: Traore Ya Ki Sakin Sojojin Najeriya da Ya Tsare, Gwamnati Ta Magantu
- Sojojin Najeriya 11 da jirgin saman soja sun shafe kwanaki uku a hannun gwamnatin sojan Burkina Faso bayan zargin keta sararin samaniya
- Ma’aikatar harkokin waje ta tabbatar da cewa ofishin jakadancin Najeriya a Ouagadougou ya soma tattaunawa da hukumomin Burkina Faso
- Hukumar sojin saman Najeriya ta ce duka ma’aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya, duk da cewa har yanzu ba a sake su sun wuce inda suka nufa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara ƙoƙarin diflomasiyya domin ganin an saki sojojin ta 11 da jirgin saman yaƙi na C-130 da gwamnatin soja ta Burkina Faso ta tsare.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton da ya bayyana cewa jirgin ya sauka a ƙasar ne bayan abin da aka kira keta dokokin sararin samaniya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa wata majiya ta tabbatar cewa sojojin da jirgin ba su samu ‘yancin wucewa ba tukuna, inda ta ce yanzu ma’aikatar harkokin waje ce ke jagorantar tattaunawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya na tattaunawa da Burkina Faso
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da cewa ofishin jakadancin Najeriya a Ouagadougou ya fara tattaunawa da hukumomin Burkina Faso.
Ya bayyana cewa:
“Ofishin jakadancin Najeriya da ke Ouagadougou yana tattaunawa da hukumomin ƙasar domin ganin an sake su.”
Rahotanni sun kuma nuna cewa sojojin sun shiga rana ta uku a tsare tun bayan da aka tilasta jirgin C-130 sauka, duk da bayanin NAF cewa jirgin ya yi “saukar gaggawa” ne bayan gano matsalar fasaha a kan hanyar zuwa Portugal.
Yadda Burkina Faso ta bayyana lamarin
Hukumar labaran ƙasar ta wallafa bayanin AES da ke cewa binciken farko ya nuna babu izinin tashi ko wucewa cikin sararin Burkina Faso ga jirgin sojan Najeriya.
AES ta bayyana lamari a matsayin keta ikon ƙasa tana mai yin kakkausar suka ga abin da ta kira rashin mutunta iyakokin sararin samaniya na ƙasashen Sahel.

Source: Twitter
Halin da sojojin Najeriya ke ciki a Burkina Faso
A nata bangaren, rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce sojojin suna cikin koshin lafiya kuma ana kula da su yadda ya kamata a hannun hukumomin Burkina Faso.
A cewar Ehimen Ejodame,
“Matuka jirgin sun yi saukar gaggawa ne bisa ka’idar tsaro bayan gano wata matsala jim kadan bayan tashin jirgin daga Legas a ranar 8, Disamba, 2025.”
Masani kan tsaro, Zagazola Makama, ma ya tabbatar da cewa har yanzu ba a saki sojojin ba a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Jiragen Najeriya sun kai farmaki Benin
A wani labarin, kun ji cewa jirgin sojan Najeriya ya saki wuta a kasar Benin yayin da wasu sojoji suka nufi kifar da gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da kai wa kasar dauki bayan ta nemi agaji a lokacin.
Bayan fatattakar masu yunkurin kifar da gwamnatin kasar, Tinubu ya yaba wa dakarun Najeriya bisa bajintar da suka nuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


