Rigima Ta Kaure a Majalisar Tarayya kan Batun da Ya Shafi Batan Fiye da N16trn a CBN

Rigima Ta Kaure a Majalisar Tarayya kan Batun da Ya Shafi Batan Fiye da N16trn a CBN

  • Rikici ya barke a zaman Majalisar Wakilai lokacin da aka gabatar da kudirin da ya nemi a gayyato gwamnan CBN, Yemi Cardoso
  • Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya yi kokarin kwantar da hankula duk da sai da ya dauki zafi kan yan Majalisa biyu
  • Bayan kowa ya natsu, Majalisar ta amince ta gayyaci gwamnan CBN kan wasu kudi da suka haura N16trn da bankin ya ki tura wa baitul-mali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rikici mai zafi da hatsaniya ta auku tsakanin 'yan Majalisar Wakilan Tarayya yayin muhawara kan wasu kudi masu nauyi da ake zargin sun yi batan dabo a bankin CBN.

Lamarin ya faru ne bayan gabatar da kudiri da ya nemi a gayyaci gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, domin ya yi bayani kan zargin kin tura N16.3trn zuwa baitul mali.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya kwana a hannun EFCC, hukumar ta fara binciken asusun banki 46

Majalisar Wakilai.
Mambobin Majalisar Wakilan tarayya yayin da suke tsakiyar zama a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, Majalisa na zargin CBN da kin dawo da Naira tiriliyan 5.2 na rarar kudin aiki da wasu kudaden gwamnati da suka kai Naira tiriliyan N11.09tr, jimulla N16.3tr daga 2016 zuwa 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin da ya jawo rikici a Majalisa

Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati, (PAC), Hon. Bamidele Salam (PDP, Osun) ne ya gabatar da kudirin.

Ya zargi CBN da gaza tura kudaden da doka ta wajabta masa, duk da cewa kudaden mallakar Gwamnatin Tarayya ne.

Bamidele Salam ya ce wannan abin kunya ne, musamman a lokacin da ƙasar ke fama da ƙarancin kudaden shiga, tsaro, da matsalar gina ayyukan more rayuwa ga yan kasa.

'Dan majalisar ya kuma zargi gwamnan CBN da kin amsa gayyatar da kwamitin PAC ya aika masa sau da dama, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Yadda hatsaniya ta kaure a Majalisa

Rigimar ta fara ne lokacin da Hon. Ghali Mustapha Tijjani daga Jano ya gabatar da gyara a kudirin, inda ya ce maimakon a gayyaci gwamnan CBN gaban PAC, a tura shi gaban kwamitin wucin gadi ne.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya sa labule da Tinubu bayan ficewar 'yan majalisa zuwa APC

Wannan kalamai na dan Majalisar Kano bai yi wa galibin ‘yan majalisa dadi ba, inda suka ki amincewa, sannan hayaniya ta tashi.

Daga nan Hon. Ahmed Jaha (Borno, APC) ya gabatar da wani gyara daban cewa a kira Gwamnan CBN da duk hukumomin da ke da hannu a lamarin su bayyana gaban PAC.

Sai dai shi ma wannan gyara ya kara haddasa ce-ce-ku-ce, har mambobin Majalisar suka dinga ihu suna kokarin hana a karanta gyaran.

Shugaban Majalisa ya dauki zafi

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya yi ta kokarin kwantar da hankali yana cewa, "kada mu zubar wa majalisar mutunci. Duniya na kallo.”

Ya gargadi wasu mambobi, ciki har da Hon. Mark Esset, Hon. Kabir Maipalace, yana mai cewa za a tura su gaban kwamitin ladabtarwa idan suka ci gaba da tada zaune-tsaye.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas a bakin aiki Hoto: @Speaker_abbas
Source: Twitter

A karshe, Majalisar ta amince da gayyatar gwamnan CBN da hukumar da ke kula da kudaden da aka tura wa asusun gwamnatin tarayya, su bayyana a gaban kwamitin PAC a ranar 16 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan bukatar Nnamdi Kanu ta a dauke shi daga gidan yarin Sokoto

Majalisa ta gayyaci ministoci 2

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa ta soma gudanar da bincike kan yadda shirin Safe School ya lalace duk da an ware masa $30m da kuma N144bn.

Majalisar ta gayyaci Ministan kudi, Wale Edun, ministan ilimi, Tunji Alausa, da Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, domin yin bayani kan yadda aka kashe dala miliyan 30.

An tsara cewa ministocin za su bayyana a gaban kwamitin wucin gadi da aka kafa domin gabatar da cikakkun bayanai kan kudaden da aka kashe da kuma abubuwan da aka aiwatar daga 2014 zuwa yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262