Zambar N5bn: Gwamnatin Tinubu Ta Gurfanar da Tsohuwar Minista a Kotun Abuja

Zambar N5bn: Gwamnatin Tinubu Ta Gurfanar da Tsohuwar Minista a Kotun Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah a gaban babbar kotun Abuja
  • Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati ta gurfanar da ita a gaban kotu kan tuhume-tuhumen da suka shafi karkatar da dukiyar kasa
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a Hamza Mu'azu ya ba da belin Stella tare da kwace fasfo dinta domin ka da ta gudu ana cikin shari'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Aahmed Tinubu ta gurfanar da tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Sanata Stella Oduah a gaban kotu.

Gwamnatin Tinubu ta gurfanar da Stella a gaban mai shari’a Hamza Muazu na Babbar Kotun Abuja, kan zargin almundahana da ta kai Naira biliyan 5.

Stella Oduah.
Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah Hoto: @StellaOduah
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo cewa an gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhume biyar, da suka shafi zamba, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da kuma hadin baki wajen aikata laifi

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Amurka da Najeriya sun fara samun fahimtar juna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin Antoni Janar na Tarayya (AGF) kuma Ministan Harkokin Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya maka tsohuwar ministar a gaban kotu.

Tuhume-tuhume da ake wa Stella Oduah

A ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da gwamnati ke mata, ana zargin Stella Oduah da karɓar Naira biliyan 2.4 daga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta hanyar kamfanin Broad Waters Resources.

Rahoto ya nuna cewa ta karbi wadannan makudan kudi ne da sunan kudin sanya ido da kula da harkokin fasaha. Wannan al’amari ana zargin ya faru ne a Janairu 2014.

A wasu tuhumomin, an ce ta karɓi N1.6bn da kuma N839m duk ta hanyar da ta saba wa dokar Advance Fee Fraud, wacce ke yaki da damfara.

Tsohuwar minista Stella Oduah, wacce ala gurfanar tare d Gloria Odita, duka sun musanta tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu.

Kotu ta bada belin tsohuwar minista

Alkalin kotun, mai shari’a Hamza Muazu ya bada belin tsohuwar ministar saboda an santa, amma kuma ya karbe fasfo dinta, kuma ba za ta fita ƙasar waje ba sai da izinin kotu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun dura fadar Aso Rock, sun shiga ganawa da Shugaba Tinubu

Lauyan Stella Oduah shi ne Onyechi Ikpeazu (SAN), yayin da Wale Balogun (SAN) ya wakilci Gloria Odita, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Stella Oduah.
Tsohuwar minista a Najeriya, Sanata Stella Oduah Hoto: @StellaOduah
Source: Twitter

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati ke gurfanar da tsohuwar ministar kan zargin sama da fadi da dukiyar kasa.

A baya, an taba gurfanar da ita a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja amma daga bisani gwamnatin ta janye tuhume-tuhumen da take mata.

Kotu ta dage shari'ar tsohon gwamnan Anambra

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta yi zama kan shari'ar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Babbar kotun tarayya ta dage shari'ar da ake tuhumar tsohon gwamnan Anambra da karkatar da akalla Naira biliyan 4 har sai baba ta gani.

Hakan ya biyo bayan bukatar da mai kara, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), ta gabatar na neman dage shari’ar har abada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262