Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga bayan Gwabza Fada a Sokoto
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun yi raga-raga da wasu tsagerun 'yan bindiga a jihar Sokoto
- Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga fiye da guda 10 bayan sun yi artabu da su a karamar hukumar Sabon Birni
- Hakazalika, sojojin ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kwato makamai masu yawa daga hannun tsagerun 'yan bindigan ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Dakarun sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga a jihar Sokoto.
Sojojin sun samu nasarar kashe ’yan bindiga 11 tare da kwato manyan makamai da dama daga hannunsu.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hedikwatar sojojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, 9 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Sokoto
Rundunar ta ce bayan ta samu sahihan bayanan sirri, tawagar jami'anta sun kaddamar da kwanton bauna mai tsari, inda aka yi artabu mai zafi da ’yan bindigar.
Wani bangare na sanarwar da rundunar sojojin ta fitar na cewa:
“An kashe ’yan bindiga 11, sauran kuma sun tsere dauke da raunukan harbin bindiga. Sojojin sun kwato bindigogi AK-47 guda takwas, jigida guda biyar da alburusai guda 26 masu kaurin 7.62mm.”
Sanarwar ta bayyana cewa sojojin sun kaddamar da gagarumin samamen ne a kusa da kauyen Kurawa a cikin karamar hukumar Sabon Birni.
Samamen ya yi sanadiyyar tarwatsa wani mugun shirin hari da ’yan bindigar suka yi niyya su kai a kauyen Tara, wanda muhimmiyar hanya ce da ’yan ta’adda ke bi.
Sojoji sun tarwatsa mugun nufin 'yan bindiga
Rundunar sojojin ta kara da cewa wannan aikin ya hana aukuwar wani lamari na ta’addanci, tare da jefa babban cikas ga hanyar wucewar ’yan bindiga da ’yan ta’adda da ke aiki a yankin Sabon Birni, wanda ya dade yana zama cikin barazana.
Hakazalika ta ce martani cikin gaggawa da jajircewa da sojojin suka nuna ya kara tabbatar da dauriyarsu, kishin kasa, da jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Sokoto da kewaye.

Source: Original
Karanta karin wasu labaran kan sojoji
- Sabon kwamandan sojoji ya kawo tsarin kakkabe 'yan bindiga gaba daya
- Sojoji sun toshe kofofin tsiga ga 'yan bindiga a Sokoto, an hallaka tsageru
- Gaskiyar abin da ya faru a Lamurde, garin da ake zargin sojoji sun kashe mata
- Ba wasa: Janar Christopher Musa ya sha sabon alwashi bayan zama Ministan tsaro
Sojoji sun kashe na hannun daman Bello Turji
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka daya daga cikin kwamandojin hatsabibin dan ta'adda, Bello Turji a jihar Sokoto.
Hatsabibin dan bindigan mai suna Kallamu ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu haddasa tarzoma a yankin Sabon Birni, inda ya dade yana jagorantar hare-hare, garkuwa da mutane.
Mazauna kauyuka da dama a karamar hukumar Sabon Birni sun fito kan tituna suna murnar nasarar da sojojin suka samu kan yan ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

