Abin da Kiristoci Suka Fadawa Dan Majalisar Amurka da Ya Ziyarce Su a Najeriya
- 'Dan majalisar Amurka Riley Moore ya kuma yin magana game da zargin kisan Kiristoci da aka ce ana yi a Najeriya
- Moore ya ce ya ji mummunan labarin kisan al'ummar Kirista yayin ziyararsa sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Benue
- Ya ce fiye da Kirista 600,000 na rayuwa a sansanonin gudun hijira, yana kira Amurka ta kara matsa lamba kan rikicin Benue
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Ɗan majalisar wakilai na kasar Amurka, Riley Moore, ya kawo ziyara ta musamman a jihar Benue a Najeriya.
Moore ya bayyana irin tashin hankalin da ya gani kuma yaji da kunnensa game da tashe-tashen hankula da ake yi wa al’ummomin Kirista a Jihar Benue.

Source: Twitter
Kiristoci sun labartawa Moore halin da suke ciki
'Dan majalisar ya bayyana haka ne a rubutunsa a dandalin X, bayan ziyarar sansanonin ‘yan gudun hijira da ya kai a jihar.
Moore ya ce ya gana da “daruruwan Kiristoci da aka kora daga gidajensu sakamakon rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar mutuwar dangi baki ɗaya.”
Ya ce labaran da ya ji daga wadanda suka tsira za su kasance tare da shi har abada saboda tsananin tashin hankalin da ke cikinsu.
A cewarsa, wata mata ta shaida masa yadda aka kashe mijinta da ‘ya’yanta biyar gabanta, ita kuma ta tsira da ranta tare da cikin da take dauke da shi.
Wata mata kuma ta ce maharan sun cakuda iyalanta gaba ɗaya a gabanta, sannan suka yaga jaririnta suka tsere.
Haka ma wani magidanci ya ba shi labarin yadda aka hallaka iyalansa a gabansa, aka daure hannunsa har ya zama gurgu.

Source: Original
'Yawan Kiristoci da ke sansanin gudun hijira
Moore ya ce fiye da Kirista 600,000 ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira a Benue, yanki da ya shafe shekaru yana fama da rikici tsakanin manoma da kungiyoyin makiyaya masu dauke da makamai.
Ya bayyana cewa ya gana da manyan shugabannin Cocin Katolika da na kabilar Tiv, ciki har da Rabaran Wilfred Anagbe da Fasto Isaac Dugu, domin tattaunawa kan abin da ya kira yunkurin kisan kare dangi da ake yi a Benue.
Moore ya ce Amurka ba za ta yi watsi da irin wadannan labarai daga al’ummomin yankin ba.
A matsayinsa na dan majalisar wakilai, ya ce ziyarar ta kasance mai matukar amfani, inda ya gana da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da sauran jami’an tsaro a Abuja.
Sun tattauna yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas da kuma kisan jama’a a Tsakiyar kasar.
Ya ce an tattauna matakai da dama da zai tabbatar sun inganta tsaro idan aka aiwatar da su, ciki har da sabuwar rundunar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka.
Moore ya yaba da ceto daliban Katolika sama da 100 da aka yi, yana mai cewa gwamnatin Najeriya ta yi aiki tukuru a wannan fannin.
An taso Ribadu a gaba kan kujerarsa
Mun ba ku labarin cewa an taso Shugaba Bola Tinubu ya gaba da sauya mai ba shi shawara kan harkokin tsaro a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu.
Sanata Francis Fadahunsi ya bukaci Tinubu ya nada tsohon hafsan soja a matsayin NSA, yana cewa hakan ne kawai zai tabbatar da tsaro.
Fadahunsi ya yaba da nadin tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa, kuma ya ce lokaci ya yi da ake bukatar ƙwararrun sojoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


