Rashin Tsaro: Sanata Ndume Ya Yabi Shugaba Tinubu, Ya Ba Gwamnoni Shawara
- Sanata Ali Muhammad Ndume ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matakan da yake dauka a fannin tsaro
- Ndume ya bayyana cewa shugaban kasar ya nuna da gaske wajen kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Hakazalika, Sanata Ndume ya bukaci gwamnonin Arewa da su yi koyi da takwaransu na jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Ali Ndume ya yaba da azamar da Shugaba Bola Tinubu ya nuna wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Sanata Ndume, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba, 10 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ndume ya ce matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka a cikin 'yan makonnin da suka gabata wajen dakile barazanar tsaro sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa.
An sace dalibai a Najeriya
A cikin watanni biyu da suka gabata, Najeriya ta fuskanci matsalolin sace-sace da garkuwa da mutane ciki har da ɗaliban makarantar GGCSS Maga a Danko-Wasagu, a jihar Kebbi.
Hakazalika sun sace ɗaliban makarantar Katolika da ke Papiri a jihar Neja da harin da aka kai wa masu ibada a cikin wani coci a jihar Kwara.
Sanata Ndume ya yaba wa Shugaba Tinubu
Sanata Ndume ya lissafo ayyana dokar ta-baci kan tsaro, samar da masu kula da gandun daji da inganta walwalar jami’an tsaro a matsayin muhimman matakai da shugaban kasa ya ɗauka domin dakile wannan mummunan yanayi.
A cewarsa, bayan samar da isassun kuɗi, Shugaba Tinubu ya nuna niyyar ɗaukar karin jami’ai a rundunar ’yan sanda da sojojin Najeriya, jaridar The Punch ta dauko labarin.
“Na ga ci gaba a bayyane wajen yadda rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro ke aiki tare. Wannan abin yabawa ne sosai."

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
"Akwai kuma ingantuwar kayan aiki, daga sababbin makamai, kayan sawa, hular kariya, takalma, har zuwa rigunan kariya.”
- Sanata Ali Ndume
Sai dai, ya kara jaddada cewa gwamnati na bukatar saka kudade sosai, musamman wajen samar da makamai masu karfi a wuraren yaki.
“Ya kamata gwamnati ta sa muhimmanci wajen samar da karin makaman yaki. A sayi karin jirage masu saukar ungulu na yaki, a kara motocin yaki masu sulke da masu dauke da bindigogi."
- Sanata Ali Ndume

Source: Twitter
Ndume ya ba gwamnonin Arewa shawara
Sanatan ya kuma shawarci gwamnonin Arewa su koyi darasi daga na gwamna Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda ya zuba sama da N100bn wajen tallafawa rundunonin tsaro da hukumomi domin kare jihar daga ’yan ta’adda.
"Ya zuba sama da N100bn wajen taimakawa sojoji, CJTF, 'yan sanda, da sauran hukumomn tsaro."
- Sanata Ali Ndume
Tinubu ya yaba da ceto daliban Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan ceto daliban jihar Neja da jami'an tsaro suka yi.
Shugaba Tinubu ya yi maraba da ceto daliban wadanda 'yan bindiga suka sace a makarantarsu da ke karamar hukumar Agwara.
Mai girma Tinubu ya kuma umarci jami'an tsaro da su gaggauta kubutar da ragowar daliban da ke tsare a hannun 'yan bindiga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

