Matsala Ta Tunkaro Ganduje kan Ƙoƙarin Yi Wa Hisbah Kishiya a Kano, an Ja Layi

Matsala Ta Tunkaro Ganduje kan Ƙoƙarin Yi Wa Hisbah Kishiya a Kano, an Ja Layi

  • Kungiyoyin matasa a yankin Arewa da ke jihar Kano sun taso maganar neman kirkirar wata hukuma mai kama da Hisbah a gaba
  • Matasan sun soki yunkurin kafa sabuwar hukumar da za ta dauki jami’an da aka sallama, suna cewa hakan barazana ne ga jihar
  • Kungiyoyin sun ce “Gwamna Abba Kabir Yusuf kadai ke da ikon gudanarwa”, kuma duk wata sabuwar Hisbah ba ta da halaccin doka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wata hadakar matasan Arewa da kungiyoyin farar hula a Kano ta yi Allah-wadai da shirin kafa sabuwar Hisbah.

Matasan suka ce abin takaici ne shirin samar da hukumar ga jami’an da gwamnatin jihar Kano ta sallama.

An gargadi Ganduje kan neman ta kafa Hisbah
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da sabon fom din shiga Hisbah. Hoto: Alameen Muhammad, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Kafa Hisbah: An taso Abdullahi Ganduje a gaba

Shugabannin kungiyoyin, ciki har da Kwamred Abdulmumin Tijjani da Isah Abubakar, sun tabbatar da haka a cikin wata sanarwa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Hisbar Ganduje za ta jawo hallaka rayuka a Arewa,' Tsohon kwamishina ya yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suka ce neman kafa sabuwar hukumar Hisbah zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsarin doka a Kano wanda zai iya jawo matsaloli da dama a jihar.

Sun bayyana cewa wannan yunkuri “neman rikici ne da ikon mulki ba bisa doka ba” kuma zai iya girgiza tsarin mulkin Kano da kwanciyar hankali.

Matasa sun soki Ganduje da neman rigima da Abba Kabir
Gwamna Abba Kabir Yasuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

An tabbatar da ikon Abba Kabir a Kano

Kungiyoyin sun jaddada cewa “Gwamna Abba Kabir Yusuf ne kadai ke da ikon aiwatar da haka”, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada a bayanae gare shi.

Sun tunatar da cewa tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da shirin daukar jami’an da aka sallama cikin sabuwar Hisbah don karfafa dokokin ladabi a Kano.

Kungiyoyin sun ce sashe na 176(2) ya bayyana cewa gwamna na rike da dukkan ikon gudanar da mulki, don haka tsohon gwamna ba shi da irin wannan iko.

Sun tunatar da cewa akwai hukumar Hisbah ta jihar wadda dokar 2003 ta amince da ita, kuma gwamna da majalisa ke da hurumin kula da ayyukanta.

Kara karanta wannan

Sabon kwamandan sojoji ya kawo tsarin kakkabe 'yan bindiga gaba daya

Hisbah: Gargadin da aka yi wa Ganduje

Sun yi gargadi cewa kafa sabuwar runduna mai zaman kanta “ba bisa doka ba ne” domin harkar tsaro na hannun tarayya karkashin jerin ikon zartarwa na kundin mulki, cewar rahoton Blueprint.

Kungiyoyin sun kara cewa kafa rundunar mutane 12,000 “na kamanni da na sojojin banga masu zaman kansu” wanda kundin tsarin mulki ya haramta karara.

Sun zargi Dr. Ganduje da “shirya siyasa” domin raunana gwamnatin Gwamna Abba Yusuf, abin da zai iya kara zafin siyasa da tabarbarewar tsaro a yankin Arewa.

An fara raba fom din shiga Hisbah

Kun ji cewa an kaddamar da rabon takardun neman shiga sabuwar Hisbah a Kano, wacce za a kafa karkashin Gidauniyar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Jagororin sabuwar kungiyar sun ce hukumar da za su kafa ba ta gwamnati ba ce, aiki ne na sa-kai domin hidimar addini da tabbatar da gyaran tarbiyya a jihar.

Wani lauya ya soki wannan yunkuri, yana kira ga hukumar DSS da ta kama masu yada fom din saboda zargin tada hankali duba da cewa akwai hukumar a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.