Gwamnoni Sun Sanya Ƙafar Wando Ɗaya da NNPCL kan $42bn na Kudin Mai
- Sabuwar rigima ta barke tsakanin gwamnoni da kamfanin mai fetur na Najeriya watau NNPCL kan wasu makudan kudi
- Gwamnonin na zargin kamfanin da rashin tura dala biliyan 42.37, lamarin da ya kai ga umarnin zaman sulhu
- Wata hukumar bincike ta nace akwai gibin kudaden mai, amma NNPCL ta musanta hakan, tana cewa duk abin da ya dace an biya shi yadda ya kamata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin kamfanin NNPCL da 'Periscope Consulting', wadda gwamnoni ta dauka domin binciken wasu kudi.
Gwamnonin na zargin rashin tura dala biliyan 42.37 zuwa asusun Tarayya wanda ke neman zama matsala a tsakaninsu.

Source: Twitter
Abin da ke neman hada gwamnoni, NNPCL fada
Wannan rikici ya fito ne daga sababbin bayanan bangarorin biyu, wanda ya sa FAAC ta umarci yin zaman hadin gwiwa domin gano gaskiyar lamari, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton FAAC na watan Nuwambar 2025 ya bayyana sababbin takaddamar, bayan an ruwaito cewa binciken zargin rashin tura kudaden ya kara tsawaita zuwa 2024.
'Periscope Consulting' ta ce akwai makudan kudaden mai da NNPCL bata tura ba, amma kamfanin man ya dage cewa babu kudi ko kadan da ya rike.
NNPCL ta jaddada cewa duk kudaden da suka dace an turasu yadda doka ta tanada, sai dai hukumar ta ki amincewa da bayanin kamfanin gaba daya.
Hakan ya sa kwamitin FAAC ya bukaci zaman sulhu domin daidaita bayanai, yana mai cewa sabanin bayanan bangarorin biyu ya hana rufe batun da dindindin.
A farkon 2025 ma FAAC ta dakatar da zaman watanni saboda rikici kan kudin da ake zargin NNPCL bata kai asusun tarayya ba, wanda ya damu jihohi.

Source: UGC
Gwamnoni sun dauki Periscope Consulting bayan korafe-korafe game da yadda NNPCL ke sarrafa kudin mai, tallafi, rabon mai da kudin hadin gwiwa.
NNPCL, wadda yanzu kamfani ne a karkashin PIA, ya ce ana rikitar da bayanan kasuwancin ta da bincike, yana kare kansa kan duk wani zargin rashin gaskiya.
Farfesa Wumi Iledare ya ce matsalar ta samo asali ne daga tsohon tsarin NNPC kafin PIA, wanda ke da gurguwar tsarin lissafi da rashin ingantacciyar bibiyar kudade.
Ya bayyana lamarin a matsayin matsalar gado, yana mai cewa cikakken aiwatar da PIA da ingantaccen bibiyar kudade ne kadai zai hana irin wadannan rudani nan gaba.
Kwamitin FAAC ya kuma bukaci NNPCL ta fayyace yadda ta kashe kudin Frontier Exploration Fund daga 2008–2024 saboda rahoton farko bai yi cikakken bayani ba.
Har yanzu ana jiran bayanai daga NNPCL game da ainihin ayyukan da aka yi da kudaden bincike a kowanne Basin da adadin da aka kashe kansu, cewar rahoton TheCable.
Gwamnoni za su tara kudi saboda matsalolin Arewa
Mun ba ku labarin cewa gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yunkuro da nufin kawo kashen matsalar tsaron da ta addabi al'ummar yankin gaba daya.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce sun amince kowane gwamna zai rika ba da Naira biliyan 1 a kowane wata.

Kara karanta wannan
Malaman majami'u sun taru a Abuja, sun fito da gaskiya kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Ya ce za a yi amfani da kudin wajen samar da kayan aiki na zamani, daukar matasa 'yan sa-kai da sauran matakan yaki da matsalar tsaro a Arewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

