Dalibi Ya Rasa Rayuwarsa wajen Murna a Bikin Kammala Digiri a Jami'a

Dalibi Ya Rasa Rayuwarsa wajen Murna a Bikin Kammala Digiri a Jami'a

  • Wani dalibi da ke shekarar karshe jami'ar a AAU Ekpoma ya rasu a hatsarin mota yayin bikin kammala jarabawa
  • Hatsarin ya faru ne sakamakon kuskure yayin sha gaban wata mota, inda motar da ya ke ciki ta bugi tirela a tsaye
  • Hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum daya da raunuka ga wasu mutane biyar, tare da jan kunnen dalibai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo – Wani dalibi da ba a bayyana sunansa ba, da ke shekarar karshe a Ambrose Alli University (AAU), ya mutu.

Lamarin ya faru ne a garin Ekpoma, Jihar Edo, inda wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da su bayan shi da abokansa sun fita da ayarin motoci taya murnar kammala jarrabawa.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Hanyoyin da dalibai za su bi domin yin rajistar jarabawar UTME 2026

Rahotanni daga shafin Facebook na Inside Edo sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin, jim kadan bayan daliban sun fito daga dakin jarabawa.

An yi hatsarin mota a Edo
Mota ta yi rugu-rugu a haɗarin da ya kashe ɗalibai Hoto: Inside Edo
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a da lamarin ya faru a kan idanunsu sun bayyana kaduwa, ganin mummunan hadarin da ya afku, inda murna ta koma kuka.

Dalibin jami'a ya rasu a Edo

Jaridar Punch ta wallafa cewa shaidu sun ce direban motar da mamacin yake ciki ya yi yunkurin wuce wata mota cikin gaggawa.

Sun bayyana cewa a garin wannan gaggawa ne kuma buge wata babbar mota, lamarin da ya jawo mummunan hadarin da ya salwantar da rayuka.

Waɗanda suka ga faruwar al’amarin sun bayyana cewa gaggawar wucewar motar ce ta jawo hatsari.

Duk da cewa mazauna yankin sun ruga domin taimakawa, amma sun tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa.

FRSC ta tabbatar da mutuwar dalibin

Kokarin samun bayanin kwamandan hukumar FRSC na Jihar Edo, Cyril Mathew, ya ci tura a farkon lamarin saboda ba a samu kiransa ba.

Dalibi ya rasu yayin haɗarin mota
Taswirar jihar Edo, inda aka yi haɗarin mota Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai daga baya, Mathew ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya bayyana cewa mutum guda ya mutu, yayin da mutane biyar suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

"Akwai abin da ba a karya da shi": Rarara ya fadi dalilin aikin alheri a kauyensu

A cewarsa, daliban sun fito ne daga cikin ayarin mota bayan kammala jarabawa, sannan daya daga cikinsu ya yi yunkurin wuce wata mota ba tare da taka-tsantsan ba.

Lamarin ya jawo an sake jaddada wa matasa bukatar kauce jefa rayuwarsu a hadari—musamman daliban da suka gama karatu.

FRSC ta shawarce su da su guji murnar da ka iya jefa rayuka cikin hadari har ma da rasa rayuka a garin murna.

Wani dalibi ya rasu a jihar Neja

A wani labarin, mun wallafa cewa Oluwaseyi Adebayo, wanda ke aji na huɗu a sashen ilimin kiwon dabbobi, ya zame ya fada cikin tafkin kiwon kifi, inda ya rasa ransa.

Lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Agusta, 2024, lokacin da Oluwaseyi ya zame ya fada cikin tafkin, kuma babu wanda ya iya ceto shi duk da kokarin da aka yi domin yin hakan.

Mazauna yankin sun ki mika gawar marigayin nan take, suna ƙoƙarin ganin an gudanar da wasu al’adun gargajiya domin kauce wa faruwar irin wannan lamari a gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng