Bakin Wike Ya Jefa Shi a Tasko, ana So Ya Biya Naira Biliyan 40 kan Sukar Dan Siyasa

Bakin Wike Ya Jefa Shi a Tasko, ana So Ya Biya Naira Biliyan 40 kan Sukar Dan Siyasa

  • Kotun tarayya da ke FCT, Abuja ta yi umurnin liƙa takardun karar da aka shigar da Nyesom Wike a kofar ofishin FCTA
  • Wani dan siyasa a Rivers, Tonye Cole na neman N40bn kan zargin batanci da ya ce Wike ya yi masa a wata hira a gidan talabijin
  • Bayan tattabar da mika sammaci ga Wike, alkalin kotu ya dauki mataki na gaba amma ministan Abuja bai ce komai ba har yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin a kai sammaci ga ministan Abuja, Nyesom Wike, ta hanyar liƙa su a ƙofar ma’aikatar FCTA.

Wannan umarni ya fito ne daga mai shari’a M.A. Hassan a zaman da aka yi a ranar Talata, yayin da yake yanke hukunci kan roƙon da aka gabatar.

Kara karanta wannan

Manyan kasa za su taru domin kaddamar da littafi da taron tuna Buhari na farko

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Nyesom Wike yayin wani taro da ya halarta. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Rivers, Tonye Cole, ya shigar yana neman N40bn saboda abin da ya kira kalaman batanci da Wike ya yi masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Wike ya yi kalaman ne a lokacin hira da Channels Television a shirin Politics Today a ranar 18, Satumba, 2025.

Kotu ta mika wa Nyesom Wike sammaci

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a M.A. Hassan ya amince da bukatar da lauyoyin Cole suka gabatar domin kotu ta bayar da umurnin liƙa takardun sammaci a babbar kofar ofishin FCT da ke Garki, Abuja.

Wannan mataki, a cewar kotun, zai tabbatar da cewa ministan ya samu cikakken sanarwa game da shari’ar da ake yi masa.

Kotun ta ce wannan hanyar ta dace saboda yanayin da ake ciki, domin tabbatar da cewa an mika takardun yadda doka ta tanada duk kuwa da cewa ba a same shi kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

Yadda Yerima ya yi aure da abubuwan da suka faru bayan rigima da Wike

Punch ta wallafa cewa umurni yana nufin cewa daga lokacin da aka liƙa takardun, an ɗauka cewa an sanar da shi kamar yadda doka ta tanada.

Ana neman Wike ya biya N40bn

A cikin ƙarar, Cole ya ce Wike ya yi masa kalaman da ya kira “batanci, na ƙarya, masu cutarwa kuma marasa kan gado.”

Ya ce maganganun sun zarge shi da rashin gaskiya, cin hanci da rashin iya gudanar da dukiyar jama’a wanda ba zai lamunta ba.

Wannan, a cewarsa dan siyasar, ya rage masa mutunci da bata masa suna a cikin gida Najeriya da kuma wajen ƙasashen duniya.

Babbar kotun tarayya a Abuja
'Yan sanda a wajen kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lauyansa Okutepa ya ce kalaman Wike sun shafi mutuncin Cole a fannin siyasa, sana’a da rayuwar yau da kullum.

Ya ce saboda haka ne Cole ke neman kotu ta tilasta wa Wike biyan diyyar N40bn domin rama barnar da aka yi masa ta fuskar suna da matsayi.

Dage zaman shari’a da rashin martanin Wike

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 24, Maris, 2026 sai dai Wike da hadiminsa, Lere Olayinka, ba su fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

Legit Hausa ta duba shafukan su na X da Facebook, babu wani martani da ya fito daga ɓangaren ministan ko hadiminsa game da zargin.

Wike ya caccaki gwamnonin Oyo da Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ragargaji gwamna Bala Mohammed da Seyi Makinde.

Wike ya bayyana cewa gwamnoni ba su isa su kore shi a jam'iyyar PDP da ya shafe shekaru yana yi wa aiki ba.

Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyar PDP ta sanar da korar ministan Abuja da wasu masu masa biyayya a watan da ya wuce.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng