Tsohon Minista Ya Kwana a Hannun EFCC, Hukumar Ta Fara Binciken Asusun Banki 46
- Tsohon ministan shari'a, kuma surukin mariyagi Shugaba Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya kwana a hedikwatar EFCC da ke Abuja
- Abubakar Malami ya kwana a hannun EFCC ne yayin da ake amsa tambayoyi tun a yammacin Litinin har zuwa washegarin Talata
- Yanzu haka dai EFCC na binciken akalla asusun banki 46 da ake zargin suna da alaka da Malami, da wasu harkalloli na gwamnatin Buhari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya kwana a hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Abuja.
Tsohon ministan shari'ar ya kwana a hannun EFCC ne a yayin da hukumar ke ci gaba da yi masa tambayoyi kan wani bincike da ake gudanarwa a kansa.

Source: Twitter
Tsohon minista ya kwana a hannun EFCC
Wani na kusa da tsohon ministan ya tabbatar cewa Malami ya samu gayyatar EFCC a ranar Litinin, sai dai ya isa hedikwatar ne da yammaci, a cewar rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta bayyana cewa isar da ya yi da yamma ne ya sa aka ci gaba da binciken har zuwa dare, aka kuma tsare shi domin a ci gaba da yi masa tambayoyi washegari.
Majiyoyin sun kara bayyana cewa akwai asusun banki 46 da ake zargin suna da alaka da Malami, kuma su ne babban ginshikin sabon binciken da EFCC ke yi a kansa.
Rahoto ya bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon ministan zai rika komawa hedikwatar hukumar EFCC kullum domin ci gaba da amsa tambayoyi.
Abin da Malami ya ce bayan ya je EFCC
A kwanakin baya, Malami ya amsa gayyatar EFCC, inda ya je hedikwatar ya amsa tambayoyi a ranar 29 ga Nuwamba, 2025, kuma ya ce tattaunawar ta yi nasara.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Malami ya bayyana cewa “gaskiya na kara bayyana” kan abin da ya kira “zarge-zargen karya” da ake yi kansa.
"Dangane da alkawarina na ci gaba da sanar da ’yan Najeriya game da gayyatar da EFCC ta yi mini, ina mika godiya ga Allah bisa bani ikon fitowa cikin aminci.
"Tattaunawar ta kasance mai kyau, kuma na samu fitowa, haka zalika an sake sanya wani sabon lokaci domin ci gaba da tattaunawa yayin da gaskiyar da ta shafi ƙagaggun zarge-zargen da aka yi a kaina ke ci gaba da bayyana."
- Abubakar Malami.

Source: Facebook
Hada-hadar kudi 5 da aka danganta da Malami
Rahoton jaridar tun a 2023 ya nuna cewa Malami na fuskantar bincike kan manyan mu'amalolin kudi biyar da ake zargin an aikata su a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Wadannan sun hada da:
- Biyan $496m ga kamfanin Global Steel Holdings Ltd kan yarjejeniyar kamfanin karafa na Ajaokuta duk da cewa kamfanin Global Steel ya yi watsi da bukatar diyya tun da farko.
- Sayar da kadarorin da aka kwace ta hannun EFCC wanda ake zargin ba a yi bisa tsari ba.
- Batun $419m na "masu ba da shawarwari" da suka ce sun taimaka wajen biyan kudin Paris Club ga jihohi.
- Yarjejeniyar biyan $200m ga kamfanin Sunrise Power kan rikicin aikin Mambilla.
- Laifin nunka kudi wajen biyan lauyoyi a batun $321m na kudaden Abacha da aka dawo da su daga Switzerland.
Malami ya ayyana tsayawa takarar gwamna
Tun da fari dai, Legit Hausa ta ruwaito cewa, a ranar 17 ga Nuwamba, 2025, tsohon ministan shari'a, ya ayyana kudurinsa na tsayawa takarar gwamnan Kebbi a zaben 2027.
Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayyar, wanda ya fice daga jam'iyyar APC a Yulin wannan shekara, ya koma jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC.
Malami ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga takarar gwamnan ne bayan shawarwari da tattaunawa mai zurfi, kuma ya bar APC saboda halin da ta jefa 'yan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


