Bello Turji Ya Sake Bayyana, an Gano Shi da Tulin Mayaka a Sokoto
- Wasu majiyoyi sun ce an hango fitaccen dan bindiga, Kachalla Bello Turji, tare da mayaka da dama
- Hakan na zuwa ne bayan daukar lokaci mai tsawo ba a ji duriyarsa duk wasu rahotanni na cewa yaransa na kai hari
- An tabbatar da cewa an gano mayakin ne a yankin Fadamar Kanwa na Sabon-Birni a jihar Sokoto
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - A daidai wannan lokaci, rahotanni sun bayyana cewa an hango babban hatsabibi dan bindiga da ake tsoro, Kachalla Bello Turji.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano shedanin dan bindigar ne tare da wata tawagar mayaka a kusa da Fadamar Kanwa a Sokoto.

Source: UGC
Shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni kan tsaro shi ya tabbatar da haka a daren yau Talata 9 ga watan Disambar 2025 a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alwashin Christopher Musa kan Bello Turji
Bello Turji dai ya dade yana addabar mutanen yankuna da dama a jihar Sokoto da Katsina da kuma Zamfara.
Fitowarsa na zuwa ne bayan nada sabon ministan tsaro, Christopher Musa wanda aka tube daga mukamin hafsan tsaro kafin ba shi kujerar minista.
Tun kafin Christopher Musa ya bar kujerar, ya sha alwashin kawo karshen Bello Turji amma bai samu dama ba har ya sauka.
Turji ya kuma bayyana a Sokoto da tawagarsa
An ce Fadamar Kanwa na cikin karamar hukumar Sabon-Birni da ke Jihar Sokoto wacce ke fama da matsalolin tsaro.
Wannan lamarin ya tayar da hankulan jama’a, musamman ganin yadda yankin ya sha fama da hare-hare a baya.
Mazauna yankin sun ce fitowar Turji a wannan lokaci na iya zama gargadi ga sababbin hare-haren da za su iya kai hari ga kauyukan da ke zagaye.
Sun yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyinsu, domin kada a sake fuskantar tashin hankali.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Benin

Source: Original
Halin da ake ciki a yankin Sokoto
Wasu majiyoyi sun nuna damuwa cewa yawancin wadannan wuraren ba su da isasshen tsaro, wanda hakan zai iya ba wa ’yan bindigar damar kai farmaki cikin sauki.
A cewar jama’a, tilas ne gwamnati ta samar da karin runduna da kuma sa ido na sama domin dakile duk wata barazana.
Mazauna yankunan sun bayyana cewa ba za su jure sake shiga cikin halin tsoro da gudun hijira ba, suna rokon hukumomi da su dauki matakan da suka dace kafin lamarin ya sake rikidewa zuwa bala’i.
Yaran Bello Turji sun sace mata a Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa ’yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun kai wani hari na musamman inda suka hallaka mutane da sace wasu da dama a Sokoto.
Rahotanni sun ce mafi yawan mutanen da aka sace 'yan mata ne, yayin da mutum ɗaya ya jikkata sosai a harin da aka kai da dare.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
Mazauna yankin sun roƙi hukumomi su ƙara tsaro da sintiri, tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace daga hannun ’yan bindiga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
