'Allah Bai Haramta ba,' Sheikh Gumi Ya Ce Babu Laifi Yin Sulhu da 'Yan Bindiga
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce babu wata koyarwar addini ko tsarin tsaro na duniya da ke haramta tattaunawa da ’yan bindiga
- Malamin ya ce manyan ƙasashen duniya suna irin wannan tattaunawa, inda ya yi misali da tattaunawar Amurka da Dalai Lama
- Gumi ya kuma bayyana dalilin da ya sanya ya daina ganawa da 'yan bindiga tuna a 2021 da kuma alakar hakan da gwamnati
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake nanata cewa ba laifi ba ne tattaunawa da ’yan bindiga.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa yin sulhu da 'yan bindiga na da fa'ida matuƙar hakan zai hana zubar da jini kuma ya ceci rayukan al’umma.

Source: Facebook
'Al-Qur'ani bai sulhu da 'yan bindiga ba' - Gumi
Malamin ya bayyana hakan a zantawarsa da kafar labarai ta BBC, ya ce Al-Qur'ani ko Injila ba su kawo wani hani na tattaunawa da 'yan bindiga, don haka batun cewa ba a tattaunawa da su ba shi da tushe a addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Me ake nufi da cewa ba a tattauna da ’yan ta’adda? Wannan magana ina suka samo ta? Ba a cikin Injila ba, ba a cikin Al-Qur'ani ba. A zahirance ma, ba gaskiya ba ne.”
Gumi ya ce manyan ƙasashen duniya ma suna tattaunawa da ’yan tawayen da ba su da iko kan gwamnati, inda ya kawo misali da cewa:
“Amurka ta taɓa buɗe kofarta don tattaunawa da Dalai Lama a Qatar. Duka ƙasashe suna tattaunawa da 'yan tawaye. Don me za mu ce mu kadai ba za mu yi ba?”
Ya jaddada cewa tattaunawa da 'yan bindiga ba wai karfafa wa masu laifi gwiwa bane, sai dai don hana zubar da jini da kare martabar kasa.
'Ba na zuwa wajen ’yan bindiga ni kaɗai' — Gumi
Yayin yake yawan shan suka da zargi game da matsayarsa kan ayyukan ’yan bindiga, da zuwa inda suke, malamin ya ce zarge-zargen da ake yi ba su da tushe.
Ya bayyana cewa:
“Ba ni kaɗai nake zuwa ba. Ina zuwa tare da jami’an gwamnati, tare da manema labarai. Ban taɓa zuwa ni kaɗai ba, ko da sau ɗaya.”
Gumi ya kuma ce ganawarsa da 'yan bindiga ta faru ne a shekarar 2021, lokacin da ya yi ƙoƙarin haɗa ƙungiyoyin domin samar da sulhu.
“Da yake gwamnatin tarayya ta wancan lokaci ba ta son tsarin tattaunawa, daga baya aka ayyana su a matsayin ’yan ta’adda, nan ne muka yanke duk wata alaƙa da su.”
- Sheikh Ahmad Gumi.

Source: Facebook
“Matsalar tsaro ba ta yi muni ba” — Gumi
Duk da yadda masu garkuwa da mutane suka bazu a Arewacin ƙasar, har ma da wasu yankunan Kudu maso Yamma, Gumi ya ce matsalar ta yanzu ba ta kai munin lokacin da bai fara tattaunawa da 'yan bindigar ba.
A cewarsa, 'yan bindiga sun fi yawan kisan gilla da kai hare-hare a lokutan baya, sannan abubuwan da ake gani a yanzu duk da muninsu, ba su kai na baya ba, in ji rahoton Leadership.
Sheikh Gumi ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta duba hanyar diflomasiyya a matsayin muhimmiyar hanya wajen kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana addabar yankuna da dama.
'Sace dalibai ya fi sauki kan kashe sojoji' - Gumi
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya sake yin magana game da matsalar tsaron Najeriya da yadda ya kamata a shawo kanta.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce nuna cewa, a ganinsa sace dalibai “laifi ne karami” idan aka kwatanta da kashe sojoji, kalaman da ake ganin za su iya jawo ce-ce-ku-ce.
Gumi ya dage cewa, duk da yake laifi ne sace dalibai, amma dai, muninsa bai kai na kisa ba, musamman idan ya zamana cewa an kubutar da yaran cikin aminci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


