Ana Wata ga Wata: EFCC Ta Kulle Gidan Tsohon Minista, Iyalansa na Ciki

Ana Wata ga Wata: EFCC Ta Kulle Gidan Tsohon Minista, Iyalansa na Ciki

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar EFCC sun rufe gidan tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva da ke Abuja
  • Mai magana da yawun tsohon ministan, Chief Julius Bokoru ya yi wa EFCC wankin babban bargo kan rufe gidan ubangidan nasa
  • Chief Julius Bokoru ya yi ikirarin cewa an rufe gidan ne alhalin iyalin Sylva na rayuwa a ciki ba tare da hukumar ta ba su takarda ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Chief Julius Bokoru, mai magana da yawun tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya yi kaca-kaca da hukumar EFCC.

Chief Julius Bokoru ya yi wa hukumar EFCC wankin babban bargo ne bisa rufe gidan maigidansa, kuma tsohon gwamnan Bayelsa da ke Maitama, Abuja.

EFCC ta rufe gidan tsohon ministan Najeriya wanda iyalansa ke ciki a Abuja.
Hukumar EFCC da ke bincike kan wasu zarge-zarge da ake yi wa tsohon minista, Timipre Sylva. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta rufe gidan tsohon minista, Sylva

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun je har gida, sun sace ɗiyar babban malamin addini

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Bokoru ya ce abin da EFCC ta yi ya saba doka, domin an aiwatar da shi “ba tare da wata wasiƙa, sammaci, umarnin bincike, ko bin tsarin doka ba,” in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa jami’an EFCC sun zana rubutu da jan fenti “EFCC — Keep Off” a bangon gidan Sylva, abin da ya ce hakan ya yi kama da gidan wanda ya tsere daga shari’a, maimakon gidan mutumin da ya yi shekaru yana hidimta wa kasa.

Bokoru ya kara da cewa abin da yafi dagula lamarin shi ne kasancewar gidan shine wurin da ’ya’yan Sylva, ’yan uwa da ma’aikatansa suke ciki, kuma suka kasa sakat tsawon makonni saboda takurawar da EFCC ta yi musu.

A cewarsa:

“Ina tambaya, ina ake so yaran su je? Har sai yaushe za su ci gaba da rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas?”

“Ba Tinubu ne ya bayar da umarni ba” — Bokoru

Ya jaddada cewa wannan ba rashin mutuntawa ba ne kawai, har ma da abinda ya sabawa ka’idojin gudanar da hukuma a cikin dimokuradiyya.

Duk da tsananin sukar sa ga EFCC, Bokoru ya ce yana da tabbacin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da hannu a lamarin, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

“Tinubu ya dade yana mutunta doka da tsarin mulki. Wannan abin ya fi kama da wata makarkashiyar siyasar cikin gida da ake kokarin jefa gwamnatin tarayya a ciki.”

Ya gargadi hukumomin gwamnati da kada su bari a yi amfani da su wajen faɗa ko husuma ta siyasa, abin da zai iya rusa martabarsu da kuma lalata amincin dimokuradiyya, in ji jaridar The Guardian.

Bokoru ya ce abin da EFCC ta yi wa tsohon ministan bai dace ba kasancewar ya sadaukar da rayuwarsa a yi wa kasa hidima.
Timipre Sylva, tsohon ministan albarkatun man fetur da EFCC ke nema ruwa a jallo. Hoto: @HETimipreSylva
Source: UGC

“Sylva ya yi wa Najeriya hidima”- Bokoru

Bokoru ya kare maigidansa yana mai cewa Timipre Sylva ya yi hidima ga Najeriya cikin nutsuwa da kishin kasa, tun daga lokacin yana gwamna, zuwa lokacin ya kasance minista, har zuwa irin goyon bayan da yake baiwa gwamnatin Tinubu.

Ya kuma tunatar da al'umma cewa hadiman tsohon ministan da wasu ma'aikatansa, ciki har da Paganengigha Anagha, Friday Lusa Paul, Musa Mohammed na tsare har yanzu.

Mai magana da yawun tsohon ministan ya ce akwai wani jami'in dan sanda, Reuben Ayuba da aka hada aka tsare su tsawon makonni ba tare da wata hujja kwakkwara ba.

EFCC ta ayyana neman tsohon minista

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar EFCC ta ayyana tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi zazzafar addu'a kan 'yan ta'adda da masu taimakonsu

Hukumar yaki da rashawar ta baza komar kama Timipre Sylva, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Bayelsa, ne bisa zargin karkatar da kudaden gwamnati.

A cewar EFCC, Sylva ya karkatar da adadin kudin da suka kai dalar Amurka 14,859,257, wani ɓangare na jarin da hukumar NCDMB ba yar na gina matatar mai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com