'Gwanda a Sace Dalibai da a Kashe Sojoji,' Sheikh Gumi Ya Sake Yin Magana Mai Zafi

'Gwanda a Sace Dalibai da a Kashe Sojoji,' Sheikh Gumi Ya Sake Yin Magana Mai Zafi

  • Sheikh Ahmad Gumi ya ce sace dalibai laifi ne karami idan aka kwatanta da kashe sojoji, yayin da ya fayyace cewa dukkan biyun laifi ne
  • Malamin ya jaddada bukatar tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai cewa sojojin Najeriya ba za su iya magance matsalar tsaro su kaɗai ba
  • Dr. Gumi ya kuma bayyana cewa, 'yan bindigan da ake gani, Fulani makiyaya ne da suka fito daga kauyuka, ba wai wadanda suke birni ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya sake yin magana game da matsalar tsaron Najeriya da yadda ya kamata a shawo kanta.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce nuna cewa, a ganinsa sace dalibai “laifi ne karami” idan aka kwatanta da kashe sojoji, kalaman da ake ganin za su iya jawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

'Na gama yin shiru,' Matawalle ya tona wadanda ke daukar nauyin bata masa suna

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana game da sae dalibai da kashe sojoji
Sheikh Ahmad Gumi ya na gabatar da darasi a ofishinsa. Hoto: @Ahmad_Gumi/X
Source: Twitter

Sheikh Gumi ya yi magana kan sace dalibai

A wata tattaunawa da ya yi a kafar labarai ta BBC a ranar Talata, Dr. Gumi ya ce sace dalibai 'yan makaranta karamin laifi ne idan aka kwatanta da kashe sojoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi ya dage cewa, duk da yake laifi ne sace yara 'yan makaranta, amma dai, muninsa bai kai na kisa ba, musamman idan ya zamana cewa an kubutar da yaran cikin aminci.

Fitaccen malamin addinin ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta zauna taburin sasanci da 'yan bindiga domin dakile zubar da jini da kuma kawo karshen ta'addanci.

"Cewa sace karamin laifi ne a kan kashe sojojinku, wannan gaskiya ne, laifin bai kai kisa ba. Kisa ya fi muni, amma dukansu dai laifi ne. Kawai dai laifin daya ya fi na dayan girma. Ba duka laifi ne yake daukar hukunci daya ba."

- Sheikh Ahmad Gumi.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

'Sace dalibai bai kai kashe soja ba' - Gumi

Sheikh Ahmad Gumi ya buga misali da sace dalibai da aka yi a makarantar GGCSS Maga da ke jihar Kebbi, inda aka kubutar da yaran cikin aminci, yana mai cewa, wannan ya isa misali kan abun da yake magana a kai.

Malamin ya ce:

"Don haka, zan iya cewa shi ne ta'addanci ne karami, kamar dai abin da ya faru a Kebbi. Sun sace dalibai, amma sun sake su. Ba su kashe su ba."

Kalaman Gumi na zuwa ne bayan da aka sace sama da mutane 315, ciki har da dalibai 303 da malamai 12 a wata makarantar Katolika a jihar Neja.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnatin tarayya, a ranar Lahadi ta sanar da cewa an kubutar da dalibai 100, yayin da aka ce 50 sun dade da kubuta 'yan kwanaki bayan sace su.

"Laifi ne, kuma muna adduna sauran su kubuta," cewar Gumi a lokacin da aka tambaye shi ko akwai abin da zai fadawa iyayen yaran.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

Sheikh Gumi ya ce akwai bukatar a tattauna da 'yan bindiga
Sheikh Ahmad Gumi ya na gabatar da karatu a masallaci. Hoto: @Ahmad_Gumi/X
Source: Facebook

'Sojoji kadai ba za su iya ba' - Sheikh Gumi

A yaki da ta'addanci, Gumi ya ce lallai sojojin Najeriya kadai ba za su iya magance matsalar tsaro da kansu ba, yana mai cewa akwai bukatar a samar da sabuwar hanyar magance matsalar tsaron kasar.

"Muna bukatar a karfafi sojojinmu. Amma ko su sojojin suna cewa wai gudunmawar da muke bayarwa a kan ta'addanci ba ta shafi amfani da makami ba. Sojoji ba za su iya magance matsalar su kadai ba, dole ana bukatar taimakon gwamnati, 'yan siyasa da mutanen gari."

- Sheikh Ahmad Gumi.

Gumi ya kara da cewa, su fa 'yan bindigar nan Fulani makiyaya ne da suka fito daga kauyuka, ba wai Fulani na birni ba, kuma sun fara ta'addanci ne saboda abubuwan da suka faru da su a baya.

Gumi ya magantu kan masu taimakon 'yan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya ce alamu na nuna cewa wasu ƙasashe masu ƙarfi na taimaka wa ’yan bindiga ta bayan fage.

Kara karanta wannan

Sulhu da 'Yan bindiga: Sheikh Gumi ya yi wa ministan tsaro, Janar Musa martani

Ya yi nuni da cewa matsalar da ta ragu a Abuja–Kaduna da Birnin Gwari ta sake ɓullo wasu wurare, abin da ke nuna akwai lauje cikin nadi.

Fitaccen malamin Musuluncin ya ce kabilanci ya shiga matsalar tsaro, abin ya ce yana bukatar kulawa ta musamman daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com