Benin: Bidiyon ’Yan Tawaye na Harbin Jirgin Yaki da Tinubu Ya Tura Kasar

Benin: Bidiyon ’Yan Tawaye na Harbin Jirgin Yaki da Tinubu Ya Tura Kasar

  • Rundunar hadin gwiwa ta sojojin Benin, Najeriya da dakarun Faransa sun yi nasarar dakile yunkurin juyin mulki a Benin
  • Bidiyo ya nuna mayakan juyin mulki na Pascal Tigri suna harbi kai-tsaye kan abin da ake zargin jirgin yakin Najeriya ne
  • Gwamnatin Benin ta kama mutane 14, tana kuma ci gaba da farautar wadanda suka kai hari suka kuma kwace gidan talabijin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Porto-Novo, Benin - Rundunar hadin gwiwa ta sojojin Benin, Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya da dakarun Faransa sun dakile wani yunkurin juyin mulki.

An ce sojojin da ke yunkurin juyin mulkin, karkashin jagorancin Laftanar Kanal Pascal Tigri, sun nuna damuwa kan mulkin Shugaba Patrice Talon.

Yan tawaye a Benin sun harbi jirgin yakin Najeriya
Sojan da ake zargi ya jagoranci yunkurin juyin mulki a Benin. Hoto: @NigAirForce, @jacksonhinklle.
Source: Twitter

Benin: Yadda 'yan tawaye ke harbin jirgin Najeriya

Wani bidiyo da kafar yada labarai ta RT ta wallafa a X ya nuna wani jirgi a sararin sama, yayin da ake jin karar harbe-harbe da ake cewa yunƙurin bindige jirgin ne.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Benin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin goyon bayan da Najeriya ta ba Benin, akwai rahotannin cewa masu juyin mulkin sun bude wuta kan abin da ake zargin jirgin yakin Najeriaya ne.

A ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025, gwamnatin Patrice Talon ta tabbatar da cewa an yi yunƙurin juyin mulki amma sojojin gwamnati sun murkushe lamarin.

Shugaba Talon ya bayyana a talabijin yana tabbatar wa al’umma cewa “komai ya koma karkashin kulawarsa” tare da jinjinawa rundunar sojin kasar bisa jajircewa da biyayyarsu.

Jiragen sun dawo Najeriya bayan faruwar lamarin

An ji rugugin fashewa a birnin Cotonou, wanda ake kyautata zaton sakamakon luguden wuta ne, duk da cewa ba a san adadin lahani da hakan ya yi ba tukuna.

Bayanan da aka gani a taswirar jirage sun nuna cewa jirage uku sun shigo Benin daga Najeriya kafin hakan ya faru.

Rahotannin The Guardian sun ce biyu sun koma Lagos, yayin da wani ya nufi sansanin sojojin saman Kanji a Jihar Niger.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: 'Matakin da Tinubu ya dauka a Benin ya dakile barazanar da ta tunkaro Najeriya'

An yi yunkurin harbe jirgin yakin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Benin. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Patrice Talon.
Source: Facebook

Benin: An kama mutane kan yunkurin juyin mulki

A halin yanzu, jami’an tsaron Benin na ci gaba da farautar wadanda suka shirya juyin mulkin, inda Shugaba Talon ya ce sun yi garkuwa da wasu mutane.

Mai magana da yawun gwamnatin Benin, Wilfried Leandre Houngbedji, ya ce an kama mutane 14 kan yunkurin karbe mulkin.

Wani dan jarida ya shaida cewa kimanin 12 daga cikin wadanda aka kama sun shiga gidan talabijin ne domin sanar da juyin mulkin.

Masu juyin mulkin sun ce Laftanar Kanal Pascal Tigri ne ke jagoranci, amma har yanzu ba a gano inda yake ba.

Majalisa ta amince Tinubu ya tura sojoji Benin

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince domin daukar matakin tura sojoji a Jamhuriyar Benin.

Wannan mataki ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar wanda bai yi nasara ba a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu zai tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Daga bisani, majalisar ta amince bayan Tinubu ya ce Benin ta nemi tallafin jiragen yaki na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.