Barau Ya Jinjinawa Tinubu da Sojojin Najeriya bayan Dakile Juyin Mulki a Benin
- Mataimakin Shugaban Majlisar Dattawa, Sanara Barau Jibrin ya yaba wa Najeriya kan gaggawar dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin
- Sojojin Najeriya sun shiga Benin ne bayan gwamnatin kasar ta nemi taimako domin kare tsarin mulki a lokacin da wasu sojoju suka yi tawaye
- Sanata Barau, wanda mataimakin shugaba ne a majalisar kungiyar ECOWAS ya bayyana cewa ba a bukatar sojoji a mulkin kasashen Afrika
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Jibrin Barau, ya bayyana jin dadi kan yadda Najeriya ta kai agaji Jamhuriyyar Benin.
Ya ce gaggawar da Najeriya ta yi wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin matsayin muhimmin mataki na kare dImokiradiyya a yammacin Afrika.

Source: Twitter
Arise News ta wallafa cewa Sanata Barau ya fadi haka ne ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya jinjinawa sojojin Najeriya
Thisday ta ruwaito Barau, wanda Mataimakin Shugaba ne a majalisar kungiyar ECOWAS ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce Shugaban Kasan ya yi abin da ya dace da ya amsa rokon neman ahajin Jamhiruyyar Benin a cikin gaggawa.
Rahotanni sun bayyana cewa yunkurin juyin mulkin ya faru ne da safiyar Lahadi lokacin da wasu sojoji suka yi tawaye.

Source: Twitter
Sojojin a ƙarƙashin tutar Military Committee for Refoundation sun bayyana hambarar da Shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na Benin.
Sai dai a cikin awanni kaɗan, gwamnatin kasar ta nemi taimakon kasashen waje, wanda ya sanya Rundunar Sojin Najeriya ta tura jami’anta.
Sojojin Najeriya sun taimaka wa Benin
A cewar rahotanni, sojojin Najeriya sun isa Benin da kayan aiki domin tallafa wa kokarin dakile yunkurin sojojin masu tawaye.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin
A cewar Barau:
“Shugaban Najeriya ya nuna cewa ba za a lamunci mulkin soja ba a wannan lokaci. Demokiradiyya ita ce hanya mafi inganci ga kasashenmu da yankinmu.”
Barau ya ce irin tsayin daka da saurin martani da Najeriya ta nuna ya sake tabbatar da matsayin ta wajen kare tsarin mulki da zaman lafiya a yankin ECOWAS.
Ya kara da cewa majalisar ECOWAS za ta ci gaba da hadin kai don tabbatar da cewa ba a sake samun irin wannan tashin hankali a makwabtan Najeriya ba.
Sanata Barau ya ce ECOWAS za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga hadin kai, zurfafa demokiradiyya da karfafa tsaro.
Haka kuma ya bayar da tabbaci cewa za a ci gaba da aikin dakile duk wani yunkurin kawo cikas ga tsarin siyasa a yammacin Afrika.
ADC ta caccaki gwamnatin Najeriya
A baya, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa gaggawar da ta nuna wajen dakile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin a kwanakin nan.
A sanarwar da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar, jam'iyyar adawa ta zargi gwamnati da nuna sakaci wajen magance matsalolin tsaro a cikin Najeriya da gangan.
Ya ce lamarin Benin ya sake tabbatar da cewa gwamnati na da ikon ɗaukar mataki cikin gaggawa idan ta natsu — amma abin takaici shi ne ta hau dokin na ki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
