Daga 1960 zuwa 2027: Bola Tinubu Zai Kafa Tarihi Irinsa na Farko a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kafa tarihi idan ya sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a zaben 2027 da ke tafe
- Idan Tinubu ya yi tazarce har zuwa 2031, zai zama zababben shugaban kasa farar hula na farko da ya yi wa'adi biyu a tarihin Najeriya
- Muhammadu Buhari da Cif Olusegun Obasanjo da suka taba wa'adi biyu a kan mulki, dukansu tsofaffin sojoji ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2027, akwai yiwuwar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kafa tarihin da ba a taba irinsa ba a Najeriya.
Ana sa ran dai Shugaba Bola Tinubu zai nemi wa'adi na biyu a zaben shugaban kasa na 2027 duk da dai har yanzu bai fito ya bayyana a hukumance ba.

Source: Twitter
Wane tarihin Tinubu zai kafa a Najeriya?
Idan Tinubu ya yi tazarce a 2027 har ya gama a 2031, zai zama zababben shugaban ƙasa farar hula na farko tun 1960 da ya yi wa’adin mulki biyu, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tarihin dimokuradiyyar Najeriya, Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo ne kadai suka taba kammala wa'adi biyu amma dukkansu sun kasance tsofaffin sojoji.
Simon Tuleh, wani masani kan manufofin gwamnati da ke Abuja, ya ce sake zaben Tinubu zai nuna cewa dimokuraɗiyya ta girma a Najeriya kuma an fara wuce zamanin da sojoji ke katsalandan a harkokin mulki.
Tuleh ya ce:
“Idan Tinubu ya samu nasara a wa’adi na biyu, hakan zai nuna cewa mulki zai iya tafiya lafiya ba tare da katsalandan din soja ba.”
Yadda Tinubu ya samu nasara a 2023
Bola Tinubu, mai shekaru 73 a duniya, ya hau mulki a 2023 bayan tsawon lokaci a siyasar jihar Legas da rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar APC.
A wa'adinsa na farko, ana ganin Tinubu ya fi karkata kan gyara da sauya fasalin tattalin arziki, gina abubuwan more rayuwa, da farfaɗo da ilimi duk da ci gaba da hauhawar farashi da tabarbarewar tsaro.
Masu sukar gwamnati da 'yan adawa na gargaɗi kan zargin cin hanci da yiwuwar rikice-rikicen siyasa musamman batun tsarin karɓa-karɓa.
Sai dai masana na lura cewa karfin APC a majalisar dokoki da kuma karfin siyasa da Tinubu ya gina tsawon shekaru na iya sake ba shi dama.
Tinubu na iya karya tsarin tsofaffin sojoji
Idan ya samu wa’adi na biyu, zai karya tsarin da aka gani a baya, inda tsoffafn sojoji kawai, irin su Obasanjo da Buhari, kadai suka kammala wa’adin mulki guda biyu.
Tuleh ya kara da cewa:
“Wannan zai zama cika burin jaruman gwagwarmayar farar hula da suka yi fafutukar Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya.”

Source: Twitter
Tinubu ya yi maraba da ceto daliban Neja
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa biA ceto dalibai 100 daga cikin wadanda 'yan bindiga suka sace a Neja..

Kara karanta wannan
Jonathan ya samu gargadi kan yin takara, an fadi manufar masu son ya gwabza da Tinibu a 2027
Shugaba Tinubu ya yaba wa hukumomin tsaro bisa kokarin da suka yi wajen kubutar da dalibai 100 na makarantar Katolika da aka kai wa hari a jihar Neja.
Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta ceto sauran dalibai 115 da malamansu da har yanzu suke tsare a hannun ’yan bindiga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

