Najeriya Ta Yi Bayani game da Jirgi da Sojinta da ke Tsare a Kasar Burkina Faso
- Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da bayanan da suka sanya jirginta, C-130 ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso
- Tuni dai kungiyar kasashen Sahek ta AES ta bayyana lamarin a matsayin kutse, tana zargin take hakkin sararin samaniyarta
- Dakarun Najeriya 11 suna cikin koshin lafiya a kasar, kuma ana shirin ci gaba da ganin yadda za a dawo da su gida
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta yi bayani game da rahotannin da suka yadu kan saukar wani jirginta, C-130 a kasar Burkina Faso.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayanai na Hedikwatar Sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce dole ce ta sa jirgin ya sauka.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa saukar da jirgin ya Air Commodore Ehimen Ejodame ya ce jirgin ya sauka ne biyo bayan matsalar fasaha.
Jirgin saman Najeriya ya samu matsala
Punch News ta wallafa cewa rundunar tsaron Najeriya ta ce matuka jirginta sun lura da matsalar jim kadan bayan tashinsa daga Legas zuwa Portugal a ranar 8 ga Disamba 2025.
A cewar Ejodame, matukan jirgin sun dauki matakin sauka a filin jirgin saman Bobo-Dioulasso—wanda shi ne mafi kusa—domin bin ka’idojin tsaro na kasa da kasa.
Ya ce wannan shi ne tsarin da aka saba bi idan an fuskanci matsalar fasaha da ka iya shafar tsaron jirgi da ma’aikatan cikinsa.
Najeriya ta karyata zargin keta Burkina Faso
Air Commodore Ehimen Ejodame ya kuma karyata jita-jitar da ke cewa an tsare dakarun Najeriya 11 da ke cikin jirgin saboda keta sararin samaniyar Burkina Faso.

Source: Facebook
A kalamansa:
“Dukkaninsu suna cikin koshin lafiya, kuma an karbe su cikin girmamawa daga hukumomin Burkinabe.”
Rundunar ta ce ana ci gaba da shirin dawo da jirgin aiki domin ci gaba da aikinsa kamar yadda aka tsara, tare da gode wa ‘yan Najeriya bisa addu’o’i da goyon bayansu.
AES ta fusata kan saukar jirgin Najeriya
Sai dai lamarin ya jawo cece-kuce daga Alliance of Sahel States wato hadin gwiwar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso.
Kungiyar ta fitar da sanarwa a kafofin gidajen talabijin na kasashen, tana zargin cewa jirgin rundunar saman Najeriya ya shigo sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izininsu ba.
Sanarwar ta bayyana saukar jirgin a matsayin keta doka, tana mai cewa an shirya rundunonin sama domin su harbo duk wani jirgi da zai kutsa sararin samaniyarsu.
Wannan martani na zuwa ne yayin da kasashen Sahel ke ci gaba da jaddada matsayinsu na kare iyakokinsu da sararin samaniyarsu da tsauraran matakai.
Burkina Faso ta rike sojojin Najeriya
A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da cewa ta tilasta wa wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya sauka a garin Bobo Dioulasso.
Ta dauki matakin tilastawa jirgin ya sauka ne bayan zargin cewa ya shiga sararin samaniyarta ba tare da izini ba a ranar 8 ga Disamba 2025.
Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsalar gaggawa a sama, wanda ya sa matukan suka nemi sauka a mafi kusa da su kamar yadda tsari da dokar kasa-kasa ta tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


