Ma'aikata Za Su Caba: Gwamna Ya Amince a Biya Albashin Watan 13
- Ma'aikata a Oyo za su yi bukukuwan Kirsimeti na shekarar 2025 cikin walwala da sakewa bayan Gwamna Seyi Makinde ya yi musu sha tara ta arziki
- Gwamna Seyi Makinde ya ci gaba da gudanar da al'adar da ya fito da ita ta kyautatawa ma'aikatan jihar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019
- Makinde ya amince da biyan albashin wata na 13 domin ba ma'aikata damar kula da iyalansu yadda ya kamata a karshen shekarar nan ta 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gwangwaje ma'aikata yayin da ake shirin bukukuwan Kirsimeti na shekarar 2025.
Gwamna Seyi Makinde ya amince a biya ma’aikata albashin wata na 13 na shekarar 2025.

Source: Twitter
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana hakan ne a wani rubutu a shafinsa na X a ranar Litinin, 8 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Bayan kwanaki 4, an samu labarin rasuwar tsohon 'dan Majalisar Tarayya a Najeriya
Gwamna Makinde ya yi wa ma'aikata halasci
Makinde ya sanar da amincewa da biyan albashin ne a dakin taro na ofishinsa da ke Agodi, Ibadan, yayin da yake kaddamar da kwamitin majalisar gudanarwa na asibitin koyarwa na jami’ar LAUTECH, Ogbomoso.
Gwamna Makinde ya tabbatar da cewa biyan albashin wata na 13 ya kasance dabi’arsa tun bayan shiga ofis a shekarar 2019.
“A wajen kaddamar da kwamitin majalisar gudanarwa na asibitin koyarwa na LAUTECH, na tabbatar cewa bashin mafi karancin albashi da na yi alkawarin biya karshen watan Satumba, za a biya shi tare da albashin watan Disamba."
“Haka kuma za mu biya ma’aikatan jihar Oyo albashin wata na 13 kamar yadda muka rika yi tun daga 2019.”
- Gwamna Seyi Makinde
Makinde zai warware matsalar yajin aiki
Gwamna Makinde ya tabbatar wa jama’a cewa matsalar da ta sa likitocin makarantar suka shiga yajin aiki za ta warware nan gaba kadan.
Ya umarci sabon kwamitin da ya gyara sashen Oyo na asibitin cikin watanni 12, tare da tabbatar da cewa cibiyar ta koma cikakkiyar asibitin koyarwa mai aiki yadda ya kamata.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta ba da cikakken goyon bayan wajen cimma wannan buri.

Source: Facebook
Su wane ne shugabannin kwamitin?
Kwamitin na karkashin jagorancin Farfesa Banji Oyelaran-Oyeyinka da Mr. Aderemi Adediji a matsayin sakatare.
Sauran mambobin sun hada Mr. Gabriel Oyelade, Dr. Adebayo Taiwo, Mrs. Agnes Isola, Dr. Kehinde Ayinde, Farfesa Adebayo Olakulehin, Farfesa Adenike Olugbenga-Bello da Dr. Oluwajoba Olayinka.
A yayin jawabin godiya, Farfesa Oyelaran-Oyeyinka ya tabbatar wa gwamna cewa kwamitin zai yi aiki tukuru wajen ganin asibitin ya zama cibiyar lafiya ta zamani wacce za a yi alfahari da ita a fannin kiwon lafiya da koyarwa.
Gwamna ya fara biyan albashin N104,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya cika alkawarin da ya dauka kan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata.
Gwamna Hope Uzodimma ya cika alkawari, ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N104,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.
Sabon tsarin albashin ya sanya jihar Imo a matakin farko a cikin jerin jihohin da ke biyan albashi mafi girma fiye da N70,000.
Asali: Legit.ng

