Malami, Buratai, Emefiele da Wadanda Aka Yi Zargi Suna Daukar Nauyin Ta’addanci

Malami, Buratai, Emefiele da Wadanda Aka Yi Zargi Suna Daukar Nauyin Ta’addanci

  • Ana zargin wasu manya a Najeriya da tsofaffin hafsoshin tsaro da hannu a daukar nauyin ta’addanci
  • Rahotanni sun nuna binciken OSW ya gano mutane da dama da ake zargi suna da alaƙa da masu daukar nauyin ta’addanci
  • Tukur Buratai, Abubakar Malami da Godwin Emefiele sun yi magana kan zarge-zargen da ake yi musu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A kwanakin nan, an jero sunayen wasu manyan mutane a Najeriya da ake zargin suna daukar nauyin ta'addanci.

Lamarin ya sake sanya shakku duba da yadda ta'addanci ke kara karfi musamman a Arewacin Najeriya.

Buratai da Malami sun yi magana kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Tsohon minista, Abubakar Malami, Tukur Buratai da Godwin Emefiele. Hoto: Tukur Buratai, Abubakar Malami.
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya ce kusan dukkan wadanda ake zargin sun fito sun yi magana tare da barranta kansu kan saka sunayensu a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jawo zargin wasu da ta'addanci

Hakan ya samo asali ne bayan wani gagarumin aikin yaƙi da ta’addanci da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da shi a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Sunan Buratai ya fito cikin masu 'daukar' nauyin ta'addanci, ya yi martani

Zarge-zargen sun fito fili ne bayan wasu kalaman ban-tsoro da tsohon babban hafsan soja, Manjo Janar Ali-Keffi mai ritaya ya fitar.

Ali-Keffi shi ne aka nada a 2021 domin jagorantar Operation Service Wide (OSW), wata rundunar bincike ta musamman da ta haɗa jami’an tsaro daban-daban domin gano shugabannin Boko Haram, gano masu ɗaukar nauyin ta’addanci.

Sai dai a cewarsa, binciken ya gano abubuwa fiye da abin da aka yi tsammani ciki har da ɗumbin masu ɗaukar nauyin ta’addanci da ake zargin suna da alaƙa da wasu manyan jami’an gwamnati.

Ya kara da cewa ba ya zargin waɗannan manyan mutanen kai tsaye da daukar nauyin ta’addanci, amma binciken ya nuna suna da alaƙa da waɗanda aka kama.

Wadanda ake zargi da hannu a ta'addanci

Sannan akwai manyan hafsoshin soji da kuma shugabannin cibiyoyin kuɗi inda ya ce daga nan ne aka fara shirin murƙushe binciken, kare wasu mutane masu ƙarfi, da kuma yi masa shiru da karfin tsiya.

SaharaReporters ta gano cewa OSW tare da Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) sun kama wasu masu matsayi a watan Maris 2021 bayan gano hanyoyin kuɗaɗen da ke da alaƙa da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Malami: Tsohon ministan Buhari ya dau zafi bayan an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci

Wadannan bayanai ne aka miƙa wa Shugaba Buhari a watan Satumba 2021, Ali-Keffi ya ce tsohon hafsan sojoji, Janar Faruk Yahaya, ya taka rawa sosai a taron, duk da cewa daga baya aka danganta shi da wani daga cikin waɗanda aka kama.

Martanin wadanda ake zargi da ta'addanci

Daga cikin wadanda aka zarga akwai tsohon hafsan sojoji, Tukur Buratai da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.

Sai kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele da tsohon hafsan sojoji, Janar Faruk Yahaya mai ritaya da sauran manya a Najeriya.

Sai dai mafi yawansu sun karyata labarin da aka yada kansu inda suka ce an yi ne kawai domin bata musu suna.

1. Tukur Yusuf Buratai

Tsohon Hafsan Hafsoshin Sojoji, Tukur Yusuf Buratai ya fito ya yi magana kan jita-jita da ake yadawa kansa game da ta'addanci.

Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya karyata rade-radin da aka danganta shi da batun daukar nauyin ta’addanci, kai tsaye ko kaikaice.

Ya ce wannan zargi karya ne tsagwaro, bai da tushe, kuma gaba daya an kirkire shi ne domin bata masa.

Buratai ya mayar da martani kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Tsohon hafsan sojoji, Tukur Buratai. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

2. Abubakar Malami

Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya yi tsokaci bayan an ambaci sunansa cikin mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi zazzafar addu'a kan 'yan ta'adda da masu taimakonsu

Abubakar Malami ya bayyana cewa ko sau daya ba a taba gayyatarsa a ciki ko wajen Najeriya kan batun da ya shafi daukar nauyin ta'addanci ba.

Malami wanda ya taba zama babban lauyan gwamnati ya bayyana manufar da mutanen da ke yada zargin daukar nauyin ta'addancin ke son cimmawa.

Abin da Malami kan zargin hannu a ta'addanci
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami. Hoto: Abubakar Malami, SAN.
Source: Twitter

3. Godwin Emefiele

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi watsi da rahotannin da ke cewa yana daga cikin mutanen da ake zargin suna da hannu a daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Masu daukar nauyin ta’addanci su ne mutane ko kungiyoyi da ke bayar da kudi da niyyar amfani da wadannan kudade wajen tallafawa hare-haren ta’addanci.

Rahoton Channels TV ya ce Emefiele ya bayyana cewa an yada labarin ne kawai domin bata masa suna a Najeriya.

An saka Emefiele kan zargin hannu a ta'addanci
Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Source: Getty Images

An shirya fadan masu 'daukar' nauyin ta'addanci

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce ba da jimawa ba za ta fitar da sunayen mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara, Daniel Bwala ya ce ana ɗaukar matakai masu tsauri kan batun tsaro a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Ya bayyana cewa haɗin guiwar ƙasashen duniya na da muhimmanci, domin matsalar ta’addanci babba ce sosai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.