Kwana Ya Kare: Kanwar Tsohon Shugaban Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Kanwar Tsohon Shugaban Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Hajiya Talatu Abubakar, kanwar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ta riga mu gidan gaskiya
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago da wasu jami'an gwamnatin Neja sun halarci jana'izar marigayiyar a babban masallacin jihar da ke Minna
  • Bago ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayiyar da sauran 'yan uwanta tare da addu'ar Allah Ya jikanta Ya gafarta masa, ya ba su hakurin jure rashinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - An shiga jimami da alhini a jihar Neja yayin da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi rashin daya daga cikin 'yan uwansa.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa gidan Sheikh Dahiru Bauchi

Rahotanni sun nuna cewa Janar Abdulsalami, wanda ya shugabanci Najeriya a lokacin mulki soji, ya rasa kanwarsa, Hajiya Talatu Abubakar a jiya Litinin.

Janar Abdulsalami Abubakar.
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar Hoto: Auwal Lasdon
Source: Getty Images

Kanwar Janar Abdulsalami ta rasu

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Hajiya Talatu Abubakar ta riga mu gidan gaskiya a jiya Litinin, 8 ga watan Disamba, 2025 a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan marigayiyar sun tabbatar da cewa kanwar Abdulsalami ta rasu ne bayan fama 'yar gajeruwar rashin lafiya.

Bayanai sun nuna cewa an riga da an yi jana’izar marigayiya Hajiya Talatu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Babban Masallacin Minna, jihar Neja.

Mataimakin limamin babban masallacin, Malam Habibu Limawa, ne ya jagoranci sallar jana'izar Hajiya Talatu Abubakar, indadaga bisani aka kai ta makwancinta.

Gwamna Bago ya halarci jana'iza

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kasance cikin manyan bakin da suka halarci jana’izar domin yin ta’aziyya ga iyalin mamaciyar, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gwamnan Mohammed Bago ya jajanta wa tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar da dangi baki ɗaya, yana mai cewa mutuwa ƙaddara ce da kowa zai dandana.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 4, an samu labarin rasuwar tsohon 'dan Majalisar Tarayya a Najeriya

Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da tuna kyawawan halaye da lokata masu cike da alheri da suka yi tare da marigayiya, Hajiya Talatu, kana su sanya ta acikin addu'o'insu.

Gwamna Bago da Janar Abdulsalami.
Gwamna Umaru Bago da Janar Abdulsalami Abubakar a wurin jana'izar Hajiya Talatu Hoto: Niger State
Source: Facebook

Addu'ar da Gwamna Bago ya yiwa Hajiya Talatu

Gwamna Bago ya roƙi Allah S.W.T ya jiƙan marigayiyar, Ya mata rahama, ya kuma bai wa iyalin da ta rasu ta bari haƙuri da juriyar wannan babban rashi da suka yi.

Ya ce:

"Muna rokon Allah Ya jikan Hajiya Talatu, Ya mata rahama, Ya sa ta a gidan Aljannah. Allah Ya bai wa iyalan ta hakurin wannna rashi da suka yi,"in ji Gwamna Bago.

Tsohon dan Majalisa ya rasu a Sakkwato

A wani rahoton, mun kawo muku labarin rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Sakkwato kuma dagacin garin Wajake, Alhaki Muhammad Mai Lato.

An tattaro tattaro cewa Mai Lato ya rasu ne a ranar Alhamis da ta gabata, 4 ga watan Disamba, 2025 a Abuja bayan doguwar rashin lafiya kuma tuni aka masa jana'iza a Sakkwato.

Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya halarci taron addu’ar fidda'u ta uku tare da manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati, ciki har da tsohon gwamna kuma jagoran APC, Sanata Aliyu Wamakko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262