Daliban Neja Sun Fadi Halin da Suka Shiga Hannun 'Yan Bindiga bayan Shakar Iskar 'Yanci

Daliban Neja Sun Fadi Halin da Suka Shiga Hannun 'Yan Bindiga bayan Shakar Iskar 'Yanci

  • Hankula sun fara kwanciya a jihar Neja bayan an kubutar da dalibai 100 daga cikin wadada 'yan bindiga suka yi garkuwa da su
  • Daliban sun bayyana yadda rayuwa ta kasance musu a lokacin da suka kwashe suna tsare a hannun tsagerun da suka sace su
  • Sun bukaci gwamnati da ta tabbatar da samar da tsaro a makarantu domin yara su samu damar samun ilmin da ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Wasu daga cikin dalban da 'yan bindiga suka sace a jihar Neja sun shaki iskar 'yanci bayan an kubutar da su.

Ɗaya daga cikin ɗaliban da aka ceto, Florence Michael, ta bayyana cewa masu garkuwa da su sun tsare su ne a cikin daji kusa da wani kogi.

An kubutar da wasu daga cikin daliban Neja
Wasu daga cikin daliban Neja da aka kubutar Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce ta yi wannan bayani ne a ranar Litinin bayan mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya mika dalibai 100 da aka sace ga gwamnatin Neja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi maraba da ceto daliban Neja, ya ba jami'an tsaro sabon umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace daliban ne a ranar 21 ga Nuwamba daga makarantar firamare da sakandare ta St. Mary’s, Papiri, a karamar hukumar Agwara.

Nuhu Ribadu ya samu wakilcin Wing Commander Abdullahi Idi Hong a wajen mika daliban da aka ceto.

Wane hali daliban suka shiga?

Yayin da take bada labarin halin da suka shiga, Florence ta ce 'yan bindigan sun samar musu da tamfal su kwanta, sannan suka gargade su kada su yi hayaniya.

“Sun ce idan muka yi surutu za su buge mu, kuma ba za mu koma gida ba.”

.- Florence Michael

Florence ta roƙi gwamnati da ta ci gaba da kare yara domin tabbatar da tsaro a makarantu.

Yadda aka ceto dalibai a Neja

A jawabinsa, Ribadu ya bayyana cewa an ceto yaran ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Ofishin NSA, DSS, sojojin Najeriya, da sauran hukumomin tsaro.

Ya ce gwamnatin tarayya tana aiwatar da matakan gaggawa na kare makarantu a yankunan da ke da haɗari, tare da aiki da gwamnatocin jihohi da shugabannin gargajiya da na addini domin samar da tsaro na dindindin a al’ummomi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta cika alkawari, ta ceto daliban makarantar Neja 100 daga ƴan ta'adda

Ribadu ya jaddada cewa ba za a bar matsalar tsaro ta hana yaran Najeriya samun ilimi ba.

An ceto wasu daga cikin daliban da aka sace a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna Bago ya yi farin ciki

Da yake karɓar yaran, gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce ceto daliban babban abin farin ciki ne ga iyayensu da gwamnatin jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Ya gode wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa irin goyon bayan da ya bayar wanda ya ba da damar kubutar da su.

Tinubu ya yi maraba da ceto dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin cikinsa kan kubutar da wasu daga cikin daliban da 'yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Shugaba Tinubu ya yabawa jami'an tsaro bisa namijin kokarin da suka yi domin ganin cewa yaran sun dawo gida lafiya.

Hakazalika, ya umarci jami'an tsaron da su gaggauta tabbatar da cewa an ceto sauran yaran da ke tsare a hannun 'yan bindigan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng