Abin da Kwankwaso Ya Fadawa Gwamna Abba da Mukarrabansa a Abuja

Abin da Kwankwaso Ya Fadawa Gwamna Abba da Mukarrabansa a Abuja

  • Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Gwamnan Kano da mukarrabansa
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai wa Kwankwaso ziyara har gida a Abuja domin nuna masa lambar yabon da aka ba shi saboda kyakkyawan jagoranci
  • Madugun Kwankwasiyya, Sanata Kwankwaso ya yabawa gwamnan bisa irin ci gaba da Kano ke samu karkashin jagorancinsa, ya ce yana alfahari da hakan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya jagoranci tawagar gwamnatin Kano, sun kai ziyara gidan jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Tawagar gwamnatin Kano ta kai wannan ziyara ta girmamawa ga tsohon gwamnan da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Lahadi, 7 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya sa labule da Tinubu bayan ficewar 'yan majalisa zuwa APC

Gwamna Abba da Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabir Yusuf lokacin da ya kai wa jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ziyara a Abuja Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso, tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin.

Me ya kai Gwamna Abba gidan Kwankwaso?

Tsohon gwamnan kuma jagoran NNPP ya bayyana cewa ya karɓi bakuncin mai girma gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a gidansa da ke Abuja.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya je tare da tawagar gwamnatinsa domin nuna wa Kwankwaso lambar girmamawa da aka ba shi a taron NEAPS da aka gudanar a Abuja.

An dai bai wa Gwamna Abba lambar yabo ta “Distinguished Award for Visionary Leadership and Public Service Sector Reform”, bisa sauyin da ya kawo da kuma kyakkawan jagorancin da ya kafa a Kano.

Abin da Kwankwaso ya fadawa Abba

Kwankwaso ya taya Gwamna Abba murna bisa wannan gagarumar nasara da ya samu, yana mai jinjina ci gaban da jihar Kano ke samu a karkashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jingine banbancin siyasa, ya ba gwamna lambar yabo a Abuja

Madugun Kwankwasiyya ya ce:

"Ina taya Gwamna Abba murna bisa wannan nasara. Ina alfahari da irin kwararan matakai da ci gaba da Kano ke samu a ƙarƙashin jagorancinsa.”
Gwamna Abba da Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso lokacin da ya karbi bakuncin Gwamna Abba da tawagarsa a Abuja Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

'Dan NNPP ya yaba wa jagororin 2

Wani dan Kwankwasiyya, Sa'idu Abdu ya shaidawa Legit Hausa cewa irin wannan kyakkywar alaka da mutunta juna ne wasu 'yan adawa ba su son gani tsakanin Kwankwaso da Abba.

Jigon NNPP ya taya Gwamna Abba murna bisa lambar yabon da aka ba shi, yana mai fatan cewa za ta kara masa kwarin gwiwa wajen sauke nauyin da ke kansa.

Malam Sa'idu ya ce:

"Wannan ziyara ta kara nuna alakar da ke tsakanin mai girma gwamna da jagoranmu. Irin wannan girmamawa ne wasu da ba su kaunar ci gaba Kano ba su son gani.
"Gwamna Abba dan mutunci ne kuma ya san halacci, ba zai taba sauka daga hanyar da maigida ya dora shi a kai ba. Ina taya mai girma gwamna murna da fatan zai nunka ayyukan alhrin da yake yi."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi gargadi kan tsaro yayin da Ganduje ke shirin kafa Hisbah a Kano

Kwankwaso ya koka kan matsalar tsaro

A wani labarin, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a sassan kasar nan.

Kwankwaso, tsohon ministan tsaro, ya koka kan yadda al’amuran ‘yan daba, ta’addanci, rigingimun kabilanci da yaduwar makamai ke ci gaba da zama barazana a Najeriya.

Ya ce alamar da ke nuna cewa gwamnati ta gaza, ita ce yadda take barin jihohi su rika kafa kungiyoyin 'yan sa-kai ba tare da cikakken horo ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262