Bidiyo: 'Yan Bindiga Sun Kashe Matar Malamin Addini, Sun Kona Masa Gida da Mota

Bidiyo: 'Yan Bindiga Sun Kashe Matar Malamin Addini, Sun Kona Masa Gida da Mota

  • Matar faston cocin Anglican ta rasa rayuwarta yayin da ’yan bindiga suka kai hari a Anambra, suka kona gidaje da motoci
  • Mazauna garin sun ce maharan sun nufi kashe Venerable Obiese, wanda ya sha da kyar, amma suka hallaka matarsa
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da harin, ta ce akwai ƙarin mutane da suka ji raunuka, kuma an fara farautar ‘yan bindigar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - 'Yan bindiga sun kashe matar fasto na cocin Anglican a safiyar Lahadi lokacin da suka farmaki cocin Saint Andrew’s Church da ke a kauyen Isiokwe.

Legit Hausa ta fahimci cewa, kauyen Isiokwe ya na cikin gundumar Lilu, karkashin karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra, Kudu maso Gabashin Najeriya.

'Yan bindiga sun kashe matar fasto, sun kona gidaje da motoci
Taswirar jihar Anambra, inda 'yan bindiga suka kashe matar fasto. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe matar malamin addini

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

Wasu mazauna garin Isiokwe sun shaidawa jaridar Premium Times cewa 'yan bindigan sun farmaki cocin ne a safiyar Lahadi, 7 ga Disamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin, wanda ya ce 'yan bindigan sun yi nufin harbe faston, mai suna Venerable Obiese, ya ce:

"Ya tsallake rijiya da baya, amma 'yan bindigar sun harbe matarsa har lahira, sun kona gida da motarsa. Sun kuma kona motocin cocin da wasu kadarori"

Legit Hausa ta ci karo da wani bidiyo da aka dauka jim kadan bayan wannan farmaki, wanda wata QueenLady Ngozi Tessy Ekwunife ta wallafa a shafinta na Facebook.

A cikin bidiyon, an ga yadda gidan faston ya kone kurmus, sannan an ga motoci biyu da wani babur duk sun kone kurmus. Hakazalika, an ga wani bangare na cocin da aka kona.

Hare-haren 'yan bindiga a garuruwan Anambra

Rahoto ya nuna cewa gundumar Lilu da wasu garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Ihiala sun shafe lokaci suna fuskantar hare-haren 'yan bindiga.

Wasu da dama daga cikin mazauna wadannan garuruwa sun yi hijira, sun hakura da zama a gidajensu, yayin da ake zargin da ma maharan na kai harin ne don kwace garuruwan.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta sake tabo batun shari'ar Musulunci da hukumar Hisbah

A watan Satumbar 2021 ne aka taba rahoto cewa 'yan bindigar sun sace Obiora Agbasilo, dan takarar gwamna na LP a zaben jihar na 2021, kuma har yau ba a sake jin duriyarsa ba.

Karamar hukumar Ihiala dai na makwabtaka da wasu garuruwan Imo, wata jihar Kudu maso Gabas da take fuskantar hare-haren 'yan bindiga ita ma.

Rundunar 'yan sanda ta ce an tura jami'ai domin kamo wadanda suka kai harin.
Babban sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun a ofis. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun tabbatar da harin coci

Mai magana da yawun rundunar 'yan snadan Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa 'yan bindiga sun farmaki coci a Lilu, kuma sun kashe matar fasto.

A wata sanarwa da Ikenga ya fitar, rundunar 'yan sanda ta ce akwai mutanen da suka ji raunuka a wannan farmakin, in ji rahoton FRCN.

Kakakin rundunar ya ce kwamishinan 'yan sandan Anambra, Ikioye Orutugu, ya yi Allah wadai da wannan mummunan hari.

Kwamishinan ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da ba su tabbacin cewa 'yan sanda sun riga sun fara farautar maharan.

Kogi: 'Yan bindiga sun sace fasto

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kai hari a wani sabon coci da aka gina na Cherubim da Seraphim inda al'umma suka shiga dimuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun aiko sako mai tada hankali, garuruwa sama da 10 na cikin hadari

Lamarin ya faru ne a garin Ejiba da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma, inda suka kutsa cocin tare da sace Fasto da kansa.

Shaidu sun ce masu ibada sun gudu domin tsira yayin da maharan suka yi harbi tare da yin garkuwa da Fasto Orlando, matarsa da wasu mambobi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com