Mutane Sun Yi Mamaki da Uwargidan Tinubu Ta 'Kunyata' Gwamna a Bainar Jama'a
- Gwamna Ademola Adeleke ya gamu da cikas daga wurin uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu a taron cikar Ooni na Ife shekara 10 a gadon mulki
- Lamarin ya faru ne lokacin da Gwamna Adeleke ke gabatar da jawabinsa, inda aka ga yana rawa a wurin taron wanda ya gudana ranar Lahadi
- A faifan bidiyon da ke yawo a kafafen aada zumunta, an ga yadda matar Tinubu ta taka wa Gwamna Adeleke burki saboda kurewar lokaci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - An yi wata 'yar dirama a Ile-Ife, Jihar Osun, yayin taron bikin cika shekara 10 da nadin Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.
Lamarin ya faru ne lokacin sa uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta dakatar Gwamna Ademola Adeleke yana cikin gabatar da jawabi a wurin taron.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume na neman dawo da hannun agogo baya game da jakadun da Tinubu ya nada

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce an shirya taron ne domin bikin cikar Sarkin shekaru 10 a kan mulki tare da nadin Oluremi Tinubu, a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwargidan Tinubu ta nemi dakatar da Gwamna Adeleke taron wanda ya gudana ranar Lahadi, kuma bidiyon abin da ya faru ya bazu a kafafen sada zumunta.
Abin da Oluremi Tinubu ta yiwa gwamna
A cikin bidiyon da Rasaq Dolapo ya wallafa a Facebook, an ga Gwamna Adeleke yana rera waka yayin da yake jawabi ga mahalarta taron, kwatsam sai Remi Tinubu ta matsa kusa da mimbari tana nuna alamar cewa lokaci ya kure.
A cikin murya ƙasa-kasa, an ji matar shugaban kasa fada wa gwamnan cewa:
“Na ba ka minti biyar ka kammala jawabin ka. Isar da sakon ya isa haka, ka bar wakar ko kuma zan kashe makirufo.”
Wannan gajerar magana ta jawo martani daban-daban daga mahalarta taron, yayin da wasu suka barke sa dariya, wasu kuwa na mamaki.
Yadda aka kammala taron lafiya a Osun
Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, da manyan baƙi daga fadin Kudu maso Yamma da ma sauran sassan kasar nan.
An shirya bikin ne don karrama Uwargidan Shugaban Kasa bisa rawar da ta taka wajen cigaban al’ummar Yarbawa da kasa baki ɗaya.
Ko da yake an samu wannan ɗan tangarda, an ci gaba da taron ba tare da an samu wata matsala ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Source: Facebook
Har zuwa yau Litinin, bidiyon na ci gaba da janyo muhawara a shafukan sada zumunta, inda masu kallo ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yadda Remi Tinubu ta taka wa Gwamna Adeleke burki a bainar jama’a.
Gwamna Adeleke ya sa dokar hana fita
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke , ya ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a garin Igbajo, da ke ƙaramar hukumar Boluwaduro a jihar Osun.
Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin dawo da doka da oda bayan barkewar rikici a garin, wanda ya jawo tashe-tashen hankula tsakanin al'umma.
Bayan haka, gwamnatin Osun ta tura dakarun sojoji, ‘yan sanda, DSS da jami’an NSCDC domin gudanar da sintiri na awa 24 a Igbajo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

