Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Nnamdi Kanu Ta a Dauke Shi daga Gidan Yarin Sokoto

Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Nnamdi Kanu Ta a Dauke Shi daga Gidan Yarin Sokoto

  • Jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu da ke zaman daurin rai da rai a gidan gyaran hali na Sokoto, ya mika bukatar a sauya masa wajen zama a gaban kotu
  • Nnamdi Kanu ya tunkari kotu da bukatar hakan ne domin a cewarsa Sokoto ta yi nisa soaai da Abuja kuma ba zai samu damar daukaka kararaa yadsa ya kamata
  • Sai dai, alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho, ya ki amincewa da bukatar tare da bayyana dalilin da ya sa bai amince ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da wata buƙata da jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya shigar a gabanta.

Nnamdi Kanu dai ya bukaci a dauke shi daga kurkukun Sokoto zuwa wani gidan gyaran hali da ke cikin babban birnin tarayya Abuja ko jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Kotu ta yi fatali da bukatar Nnamdi Kanu
Jagoran kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu da sandar alkali Hoto: @ImranMuhdz
Source: UGC

Jaridar The Nation ta ce alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho ne ya yi watsi ds bukatar a ranar Litinin, 8 ga watan Disamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kanu ya mika kokon bararsa ga kotu

Kanu ya roki kotun da ta bayar da umarni ga gwamnatin tarayya ko hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) da su hanzarta dauke shi daga Sokoto zuwa Kuje da ke Abuja ko Keffi da ke Nasarawa.

A madadin haka, ya nemi a mayar da shi duk wani gidan gyaran hali da ke karkashin hurumin kotun, ciki har da Suleja ko Keffi, domin ya samu damar bin diddigin shari’arsa yadda ya kamata.

Me alkali ya ce kan bukatar Kanu?

Sai dai a ranar Litinin, Mai Shari’a James Omotosho ya ki amincewa da bukatar da jagoran na kungiyar IPOB ya gabatar, tashar Channels tv ta dauko labarin.

Mai shari'a James Omotosho ya bayyana cewa ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba sai an saurari bangaren gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

'Abin da ka shuka': Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Alkalin ya umurci Kanu da ya maida bukatar zuwa kudirin da za a iya sanarwa domin a tura wa dukkan ɓangarori, ta yadda za a ji daga bakinsu.

Daga nan sai mai shari’a Omotosho ya sanya ranar 27 ga Janairu, 2026, domin sauraron bukatar.

Kotu ta yi watsi da bukatar Kanu
Mazi Nnamdi Kanu a cikin kotu tare da lauyoyi Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Kotu ta samu Kanu da laifi

A ranar 20 ga Nuwamba, kotun ta samu Kanu da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da suka shafi ta’addanci da gwamnatin tarayya ta gabatar, tare da yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.

Daga nan aka tura shi gidan gyaran hali na Sokoto saboda damuwar tsaro a Kuje, wanda a baya 'yan ta'adda suka taba fasawa.

Gwamnan Sokoto ya musanta ziyartar Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan rahotannin dake cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya ziyarci Nnamdi Kanu, tare da takwaransa na jihar Abia, Alex Otti.

Gwamnatin ta karyata rahotannin da ke cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya raka takwaransa na Abia, Alex Otti, yayin ziyarar da ya kai wa Nnamdi Kanu, a gidan gyaran hali na Sokoto.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Ta bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu ba ya cikin Najeriya lokacin da Gwamna a.Alex Otti ya zo jihar Sokoto.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng