Shugaba Tinubu Ya Jingine Banbancin Siyasa, Ya ba Gwamna Lambar Yabo a Abuja
- An karrama Gwamna Dauda Lawal da lambar yabo bisa yadda ya gyara harkokin shugabanci da tunkarar matsalar tsaro a Zamfara
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya mika wa gwamnan lambar yabon a madadin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa wannan karramawa za ta kara wa Gwamna Lawal kwarin gwiwa wajen inganta rayuwar al'umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika lambar yabo ta Nigeria Excellence Awards in Public Service (NEAPS) 2025 ga Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
An ba Gwamna Lawal wannan lambar yabo ne saboda shugabanci da kokarin magance matsalar tsaro a jiharsa da ta jima tana fama da matsalolin 'yan bindiga.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa an gabatar da lambar yabon ne a daren Lahadi a Abuja, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya wakilci shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da yasa aka zabi Gwamna Lawal
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, kungiyar The Best Strategic Media (TBS) tare da hadin gwiwar Ofishin SGF ne suka shirya taron.
Sanarwar ta bayyana cewa NEAPS, wanda aka kaddamar a shekarar 2022, tana girmamawa tare da karrama mutanen da suka bayar da gudunmuwa mai dorewa a fadin kasa.
A cewar sanarwar:
"An karrama Gwamna Lawal saboda gagarumin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a fannoni daban-daban na jihar Zamfara.”
Wasu nasarorin Gwamna Dauda Lawal
Daga cikin manyan nasarorin da aka ce gwamnan ya samu akwai gyara tsarin aikin gwamnati da jin dadin ma’aikata da biyan fiye da N15bn na bashin fansho ga tsofaffin ma'aikata.
Haka zalika Gwamna Lawal ya aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000, sannan ya biya bashin albashin watanni 13 da ma'aikata suke bi.
A bangaren ilimi da lafiya, gwamnan ya gyaran makarantu sama da 500, gina wasu sababbi, da samar musu da kayan aiki na zamani, sannan ya gyara asibitocin gwamnati, tare da samar musu da kayan aiki.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro
Bugu da kari, sanarwar ta ce Gwamna Lawal ya kafa rundunar askarawan Zamfara (CPG) tare da ba jami’an tsaro motocin aiki da man fetur don samar da tsaro a Zamfara.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya kara da cewa:
"Wannan karramawa za ta kara wa gwamna kwarin gwiwa wajen ci gaba da kokarin cetowa da gina sabuwar jihar Zamfara.”
Ana jita-jitar gwamnan Zamfara zai koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa an fara yada jita-jitar cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara zai sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki.
Sai dai jita-jita ta nuna cewa akwai sharuddan da gwamnan yake so a cika masa kafin ya amince ya koma APC tare da magoya bayansa.
An ruwaito cewa Gwamna Dauda ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a birnin Faris, Faransa, tare da gwamnonin Enugu da Taraba, inda ya bayyana shirinsa na komawa APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
