Gwamnatin Kebbi Ta Ware N10bn don Ceto Kujerun Aikin Hajjin Maniyyatan Jihar
- Gwamnatin Kebbi ta ware Naira biliyan 10 domin samun karin kujerun aikin hajjin bana 1,300 ga maniyyatan jihar
- An tsawaita wa’adin biyan kudin Hajj zuwa 16 ga Disamba, wanda hakan zai ba wa duk maniyyata damar samun kujerunsu
- Hukumar Hajj ta Kebbi ta riga ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, tare da tabbatar da cewa kowa zai samu damar sauke farali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 10 domin samun kujeru 1,300 na karin Hajj ga ‘yan jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan wa’adin da Hukumar Kula da Hajj ta Kasa (NAHCON) ta kafa na 5 ga Disamba, 2025 ga maniyyatan kasar nan su biya kudinsu.

Kara karanta wannan
Kotu ta yi hukunci kan bukatar Nnamdi Kanu ta a dauke shi daga gidan yarin Sokoto

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaban Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruku Aliyu-Yaro, ne ya bayyana haka.
Za a kara yawan kujerun hajjin Kebbi
FRCN ta wallafa cewa Alhaji Faruku Aliyu Yaro ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi cewa rancen ya taimaka wajen cike gibin kujerun da ake bukata.
Ya kara da cewa wannan ya taimaka wajen kare dukkanin kujerun da aka ba wa jihar, kuma babu maniyyacin da zai rasa kujerarsa ta bana.

Source: Facebook
Ya kuma yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa yadda ya tsoma baki da nuna tausayi da kula wa ga jama’a.
Aliyu-Yaro ya ce:
“Da dama daga cikin masu niyyar aikin Hajj sun riga sun shiga yanayi mara dadi saboda sun dauka za su rasa damar akin hajjin bana. Amma Gwamna ya shiga lamarin a lokacin da ake bukata. Ya cancanci addu’o’i na musamman daga al’ummar Kebbi.”
Ana ci gaba da shirin aikin hajji
Shugaban hukumar ya kara da cewa wa’adin biyan kudin Hajj yanzu ya tsawaita zuwa 16 ga Disamba, wanda hakan ya bude kofar ga duk masu niyya su biya N7,696,769.79 a hankali.
Dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar za su amfana daga wannan tsawaita wa’adi, wanda ya tabbatar da cewa kowa zai samu damar da ake bukata.
Faruku Aliyu Yaro ya bayyana cewa hukumar ta riga ta fara shirye-shiryen da suka shafi aikin Hajj na 2026.
Shugaban hukumar aikin hajjin ya tabbatar da cewa Kebbi ta soma shiri kimanin watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata.
Ya jaddada:
“Muna son kowane mazaunin jihar—ko daga Argungu, Yauri, Zuru, ko Bagudo—ya samu dama. Babu wanda ya yi niyyar Hajj da za a bari a baya.”
NAHCON ta fitar da ka'idojin aikin hajji
A baya, mun wallafa cewa hukumar Kula da Hajjin Najeriya (NAHCON) ta sanar da jerin sababbin ka’idoji da matakai da za su jagoranci aikin Hajjin shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya 'wawure' Naira biliyan 16.5 na gyaran gadar Arewa? Gaskiya ta fito
adannan sababbin ka'idoji sun fara daga kan tikitin jirage, tsare-tsaren tafiya da sharuddan kiwon lafiyan 'yan Najeriya a aikin hajjin da ke tafe a shekara mai zuwa.
Sanarwar ta fito ne a ranar 4 ga Disamba, 2025, bayan wani taro da aka gudanar tsakanin shugabannin alhazai na jihohi da manyan kamfanonin jiragen sama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
