'Yan Bindiga Sun Bude Wuta a tsakiyar Kasuwa, Sun Kashe Mutane
- Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai mummunan hari a kasuwar Afor da ke Nawfia, inda ake zargin mutane da dama sun mutu
- Shaidun gani da ido sun ce maharan sun bude wuta ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsananin tsoro da rudani
- Shugabannin al’umma sun tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga hukumomi da su kara tsaro domin hana aukuwar irin haka a nan gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra – Tsautsayi ya afka wa al’ummar Nawfia da ke cikin karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari kasuwar Afor a daren Lahadi.
Shaidu daga yankin sun bayyana yadda maharan suka bayyana cikin gaggawa tare da bude wuta kan jama’a ba tare da wata sanarwa ba.

Source: Original
Leadership ta bayyana cewa farmakin ya jefa mazauna yankin cikin tsananin firgici, inda wasu suka mutu a wurin, wasu kuma suka tsere domin ceton rayukansu.
Shugaban kungiyar Nawfia Progressive Union, Cif Daniel Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumomin tsaro sun fara bincike.
Harin ya jefa jama’an yankin a firgici
Mazauna yankin sun bayyana yadda suka shiga ruɗani da tashin hankali bayan ganin maharan sun dura kasuwar cikin wani salo.
Wani mazaunin yankin ya ce:
“Maharan sun shigo kasuwar Afor cikin gaggawa sannan suka fara harbe-harbe, mutanenmu da dama sun mutu. Babu wanda ya san dalilin wannan hari, al’ummarmu ta gigice matuka.”
Wasu mazaunan sun bayyana cewa su ma har yanzu ba su farfado da firgicin da suka shiga ba, inda suke ci gaba da rokon gwamnati da hukumomin tsaro su kara tsaro a yankin don hana maharan sake dawowa.
Hukumomi sun fara bincike kan lamarin
Punch ta ce wani jami'in dan sanda da bai bayyana sunansa ba ya ce bincike ya fara domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Ya ce:
“’Yan sanda sun fara bincike, kuma zamu tabbatar an kamo wadanda suka aikata wannan ta’addanci. Mun yi Allah wadai da wannan danyen aiki sannan muna tabbatar wa jama’a cewa za a gurfanar da masu laifin.”

Source: Facebook
Hukumomi sun ce suna daukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa wannan hari bai sake faruwa ba, tare da kara fadakar da al’umma su kasance masu lura da duk wani motsi da ba a saba gani ba.
Shugabanni sun yi Allah-wadai da harin
Shugaban kungiyar Nawfia Progressive Union, Cif Daniel Okoye, ya fitar da sanarwa daga bisani yana bayyana matukar bakin cikinsa kan abin da ya faru.
“Na samu wannan mummunan labari cikin matukar baƙin ciki. Al’ummar mu ta yi rashi.”
Kwankwaso ya yi magana kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tsaro ya kara dagulewa a Najeriya.
A bayanin da ya yi, Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki dakile yaduwar makamai a hannun jama'a.
Baya ga haka, Rabiu Kwankwaso ya yi zargin cewa wasu 'yan siyasa sun fara amfani da damar kafa rundunar sa-kai domin cimma manufa ta dabam.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


