ECOWAS Ta Tura Zaratan Sojoji Benin daga Najeriya da Wasu Kasashe 3

ECOWAS Ta Tura Zaratan Sojoji Benin daga Najeriya da Wasu Kasashe 3

  • Kungiyar ECOWAS ta amince da tura rundunar tsaro zuwa Jamhuriyar Binin bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar
  • Hakan ya biyo bayan taron gaggawa na shugabannin ƙasashen yankin da ya tabbatar da buƙatar kare tsarin mulki a Benin
  • An ce rundunar za ta haɗa sojoji daga kasashen Najeriya, Saliyo, Côte d’Ivoire da Ghana domin taimakawa sojojin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar ECOWAS ta sanar da tura rundunar tsaro zuwa Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulki da dawo da zaman lafiya bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

An ce matakin ya nuna jajircewar ƙungiyar wajen kare dimokuraɗiyya da dakile duk wani yunƙurin kifar da gwamnati a yankin yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya tura sojoji Benin suka fatattaki masu son juyin mulki

Taron shugabannin ECOWAS
Tinubu da wasu shugabanni a taron ECOWAS. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sanarwar da ECOWAS ta fitar a X ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa tanade-tanaden kundin ƙungiyar, musamman Sashe na 25(e) na yarjejeniyar 1999 da ta shafi magance rikici, sulhu da kiyaye zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tura dakarun ya zo ne bayan shawarwari tsakanin ƙasashe mambobi ta hannun majalisar sulhu, a matakin shugabannin ƙasashe da gwamnatoci, inda shugaban ECOWAS ya bada umarnin tura rundunar.

Kasashen ECOWAS da suka tura sojoji Benin

A cewar ECOWAS, rundunar za ta haɗa dakarun Najeriya, Saliyo, Côte d’Ivoire da Ghana, waɗanda za su yi aiki kafa-da-kafa da gwamnatin Benin da rundunar sojan ƙasar domin tabbatar da tsaro.

Kungiyar ta ce haɗin gwiwar na nufin dawo da zaman lafiya da kuma kare tsarin da al’ummar Benin suka zaba a cikin shekaru 35 da suka shafe ba tare da juyin mulki ba.

Tinubu da shugaban kasar Benin
Bola Tinubu da shugaban Benin da aka so kifarwa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ƙasar Binin ta shiga cikin rudani ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin Colonel Pascal Tigri suka yi yunkurin hambarar da gwamnatin Patrice Talon, suka mamaye tashar talabijin ta ƙasa tare da bayyana cewa sun kwace mulki.

Kara karanta wannan

'Kisan Kiristoci': Tawagar Amurka ta shigo Najeriya, ta yi magana da Ribadu

Tasirin matakin ECOWAS a Benin

Rundunar haɗin gwiwar da za a tura za ta mayar da hankali kan tallafa wa dakarun Binin wajen tsare manyan cibiyoyin gwamnati, hana yaduwar tawaye, da gudanar da sintiri don tabbatar da cewa tsarin mulki ya koma kamar yadda ake so.

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa ECOWAS ta bayyana cewa matakin yana da muhimmanci domin hana sake yunkurin juyin mulki ko tashe-tashen hankula a ƙasar ko ma a yankin gaba ɗaya.

Baya ga haka, ƙungiyar ta ce rundunar za ta yi aiki cikin umarnin gwamnatin Benin, tare da kula da muhimman wurare da kuma tabbatar da cewa al’ummar ƙasar sun koma cikin kwanciyar hankali bayan tashin hankalin da aka samu.

Sojojin Najeriya sun kai dauki Benin

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa dakarun Najeriya da suka kai dauki kasar Benin.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a bisa umarninsa sojojin Najeriya suka tafi Benin domin kare dimokuradiyyar kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin

Fadar shugaban kasa ta bayyana yadda sojojin Najeriya suka fatattaki masu yunkurin juyin mulkin cikin kankanin lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng