Gwamnati Ta Cika Alkawari, Ta Ceto Daliban Neja 100 daga Ƴan Ta'adda
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sako dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a makarantar St. Mary’s Catholic da ke Jihar Neja
- Rahotanni sun ce tsauraran samame na soji, sintirin jiragen sama da taimakon masu farautar daji ne suka taimaka wajen kubutar da yaran
- Duk da wannan cigaba, jami’an makarantar da iyaye sun ce ba a sanar da su a hukumance ba, amma suna jira
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Gwamnatin tarayya ta samu nasarar ceto yara 100 daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su daga makarantar St. Mary da ke Papiri.
Ceto yaran makarantar da aka sace daga Karamar Hukumar Agwara a Jihar Neja na zuwa ne makonni biyu bayan sace su da jefa jama'a a cikin tashin hankali.

Source: Facebook
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar wa TheCable cewa an sake yaran kuma suna cikin koshin lafiya a yanzu haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ceto daliban Neja
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewar majiyar, cikakkun bayanai game da yadda aka sako su na nan tafe a hukumance nan da Litinin.
Ƴan bindigan sun kai farmaki makararantar ne da 2.00 na safe a ranar 21 ga Nuwamba, inda suka sace mutum 315 — ciki har da dalibai 303 da malamai 12.
Daga baya, dalibai 50 sun tsere cikin awanni 24 na farko, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka rage a hannun masu garkuwar zuwa 265.

Source: Twitter
An ce ceto daliban ya biyo bayan tsattsauran matakan soji, sintirin jiragen sama a jihohin Neja, Kwara da Kebbi da kuma tura farauta daji domin bin sawun ’yan bindigan.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ma ya soke wasu tafiye-tafiye na ƙasashen waje domin sa ido a kai tsaye kan matakan ceto daliban.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci
Lamarin ya sa gwamnati ta rufe makarantun Jihar Neja da wasu cibiyoyin tarayya da ke yankunan barazana.
Iyayen daliban Neja na jiran sanarwar gwamnati
Sai dai a bangaren makarantar, Daniel Atori, mai magana da yawun shugaban kungiyar CAN na jihar Neja, Bulus Yohanna, ya ce jami’an makarantar ba su samu wata sanarwa game da sakin yaran ba.
A Kalamansa:
“Makarantar ba ta samu bayanai ba. Bishop, wanda shi ne mai makarantar ma ba a sanar da shi ba. Haka iyayen yaran ma, babu wanda ya ji komai. Ba mu tabbatar ba tukuna."
Ya ce duk da haka, idan labarin gaskiya ne, zai zama abin farin ciki sosai, domin sun dade suna addu’a da jiran dawowar yaransu.
Ya kara da cewa har yanzu suna jiran sanarwa daga gwamnati a hukumance yayin da adadin wadanda ke tsare ya rage dalibai 153 da malamai 12.
Daliban Neja sun gudo gida
A baya, kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban makarantar Katolika da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sun samu nasarar tserewa daga yan ta'adda.
Rahotanni sun e tuni daliban da aka sace a harin da aka mai makarantarsu suka koma gidajensu kuma suna cikin koshin lafiya yayin da sauran daliban ke hannun masu garkuwa da mutane.
Wannan na zuwa makonni bayan mummunan harin da ya girgiza al’ummar Papiri da ke ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da malamai na makarantar St. Mary’s Catholic.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

