'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani kan Liman da Masu Sallah a Sakkwato? An Samu Bayanai
- Rahoton da ake yadawa cewa 'yan bindiga sun kai farmaki wani masallaci a karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sakkwato ba gaskiya ba ne
- Shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu ya ce babu wani hari da aka kai masallaci har aka kashe liman
- Sai dai mazauna kauyen Gatawa sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane biyar da sace wasu da dama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Wasu rahotanni da aka fara yadawa sun yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun kai mummunan hari kan musulmai a masallaci a jihar Sakkwato.
Rahoton ya nuna cewa maharan sun kashe limamin masallacin da wasu masallata a yankin karamar hukumar Sabon Birni.

Source: Original
Dagaske an kai hari masallacin Sabon Birni?
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, ya yi watsi da wannan labarin, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu kafafen yada labarai na yanzar gizo sun rawaito cewa ’yan bindiga sun shiga masallaci a Sabon Birni inda suka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu amma shugaban karamar hukumar ya ce labarin ba shi da tushe.
A wata tattaunawa ta waya, Hon. Ayuba Hashimu ya ce:
“Ban san wani masallaci da aka kai wa hari ba, balle har a ce an kashe Liman da masallata. Labarin ƙarya ne gaba ɗaya.”
Dan Majalisar Wakilai ma ya musanta
Haka zalika, wani dan majalisa daga yankin, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar cewa babu wani harin masallaci da ya faru a ranar Asabar.
“Ban san daga inda suka samo labarin ba, amma ba gaskiya ba ne. Babu wani masallaci da aka kai wa hari,” in ji shi.
Sai dai a wani harin daban da ya faru da safiyar yau Lahadi a kauyen Gatawa, cikin wannan karamar hukuma ta Sabon Birni, mutane biyar sun rasa rayukansu sannan mutum ɗaya ya ji munanan raunuka.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya 'wawure' Naira biliyan 16.5 na gyaran gadar Arewa? Gaskiya ta fito
Yan bindiga sun kashe mutum 5
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun shiga garin da tsakar dare, misalin karfe 1:30 na dare, kuma daga zuwa suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
"’Yan bindigar sun kai hari kauyen da misalin 1:30 na dare, suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.’Yan sa-kai sun yi kokarin tarbarsu, aka yi musayar wuta da su.
"’Yan sa-kai hudu sun mutu nan take, biyu sun ji raunin harbin bindiga aka kai su asibiti, amma ɗayansu daga baya ya rasu,” in ji shi.
Ya ce ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutane shida, ciki har da matan aure biyu, ’yan mata biyu, da yara maza biyu, sannan sun tafi da dabbobin jama'a, in ji Leadership.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun yi barazana a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa mazauna kauyuka fiye da 12 da ke yankin karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato sun shiga tashin hankali da zaman dar-dar.
'Yan bindiga sun jefa mutanen wadannan garuruwa cikin tashin hankali da fargaba bayan turo wani sako da ke barazanar kawo masu farmakin rashin imani.
Barazanar 'yan bindigan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Arewa, musamman bayan hare-haren da aka kai jihohin Kebbi, Kwara da Neja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

