Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Matakai 3 bayan Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki a Benin

Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Matakai 3 bayan Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki a Benin

  • Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da yunurin juyin mulki da sojoji suka yi a Benin, tana mai yabon matakan gaggawa aka dauka
  • Wasu matakai da Najeriya ta dauka sun hada da tura jiragen yaki zuwa sararin samaniyar Benin don dakile duk wata barazana ga kasar
  • Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da aiki tare da Benin da sauran kasashen ECOWAS domin hana sake bullar irin wadannan rikice-rikice

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki matakai bayan da sojoji suka yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2025.

Gwamnatin Najeriya dai ta bayyana cewa wannan yunkuri na juyin mulki hari ne kai tsaye kan tsarin dimokuradiyya da zabin al’ummar kasar Benin.

Kara karanta wannan

Najeriya ta janye jirgin yakinta zuwa Benin bayan sanin halin da ake ciki

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakai bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyyar Benin
Shugaba Bola Tinubu ya tura jiragen yaki zuwa Benin bayan yunkurin juyin mulki. Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, Najeriya ta tabbatar da goyon bayanta ga gwamnatin Patrice Talon da mutanen kasar bakidaya, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Najeriya ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan gwamnatin Jamhuriyar Benin, kuma muna yabawa da matakin hukumomin tsaro wajen kare kundin tsarin mulki da tabbatar da zaman lafiya.”

An kuma jinjinawa sojojin Benin saboda bajintar da suka nuna wajen dakile masu yunkurin kifar da gwamnatin Patrice Talon.

Matakai 3 da gwamnatin Tinubu ta dauka

1. Najeriya ta yi kira ga kasashe

Sanarwar ta kara da cewa duk wani yunkurin sauya gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba barazana ce ga kwanciyar hankali a yankin, kuma tana taba dimokuradiyya.

Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa:

“Gwamnatin Najeriya na kira ga dukkan kasashen duniya su dage wajen kare dimokuradiyya, su kuma tabbatar da bin yarjejeniyoyi na ECOWAS da AU kan mulkin dimokuradiyya da kwanciyar hankali.”

Kara karanta wannan

Sunaye da bayanan kasashen Afrika 8 da sojoji suka yi juyin mulki a shekaru 5

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta kuma bukaci ’yan Benin su ci gaba da bin doka, tare da kai duk wata bukata ta siyasa ta hanyar lumana ba tashin hankali ba.

2. Najeriya ta tura jiragen yaƙi

A gefe guda, wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa rundunar sojojin Najeriya ta tura jiragen yaki zuwa sararin samaniyar Benin bayan rahotannin kifar da gwamnati.

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa jiragen sun tashi daga Lagos domin gudanar da sintiri a saman Benin, da nufin tantance tasirin lamarin ga tsaron Najeriya.

Wani babban jami’in tsaro ya bayyana cewa:

“Jiragen sun isa Benin. Najeriya na bibiyar al’amura sosai domin kare muradunta da sanin ko akwai barazana ga iyakokinta.”
An rahoto cewa gwamnatin Najeriya ta tura jirgin yaki zuwa Benin domin dakile duk wata barazana ga kasa
Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya. Hoto: @NigAirForce
Source: Facebook

3. An janye jiragen yaƙin Najeriya

Daga bisani, majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa Najeriya ta umarci jiragen da su komo gida bayan samun rahotanni cewa an shawo kan yunkurin juyin mulkin, kamar yadda muka ruwaito.

An janye jiragen da ke sintiri ne da rana bayan an tabbatar cewa babu wata barazana kai tsaye ga iyakar Najeriya, in ji rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi halin da ake ciki bayan yunkurin juyin mulki a Benin

Wata majiya ta ce:

“Bayan sababbin bayanan sirri da muka samu, an tabbatar da cewa tsaro ya daidaita, kuma babu barazana ga Najeriya. An umarci jiragen su dawo gida.”

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewa za ta ci gaba da aiki tare da Benin da sauran kasashen ECOWAS domin tabbatar da zaman lafiya da hana sake bullar irin wadannan rikice-rikice.

2022-2025: Juyin mulki a kasashen Afrika 8

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya sake jefa nahiyar Afrika cikin fargaba, yayin da sojoji suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

Duk da sanarwar juyin mulki da sojojin suka yi, fadar kasar Benin ta tabbatar da cewa Talon yana cikin koshin lafiya, kuma rundunar sojin kasa, mai biyayya ga dimokuradiyya ta fara dawo da ikon ta.

Wannan yunkurin ya kara shiga jerin juyin mulki da dama da suka yiwa Afrika katutu cikin shekaru biyar, ciki har da juyin mulki a Nijar, Madagascar, Burkina Faso da wasu kasashe biyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com