Najeriya Ta Janye Jirgin Yakinta zuwa Benin zayan Sanin Halin da Ake Ciki
- Kasar Najeriya ta sake tunani bayan tura jirgin yakinta da ke shawagi a Jamhuriyar Benin da aka ce an yi juyin mulki
- Najeriya ta janye jiragen yaƙinta ne daga kasar bayan hukumomi sun tabbatar da cewa komai ya lafa
- Sojoji masu biyayya ga Shugaba Patrice Talon sun ce sun kwace birnin Cotonou da kafafen yada labarai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Majiyoyi sun tabbatar da cewa kasar Najeriya ta janye jirgin yaƙin da ta tura Jamhuriyar Benin.
Hakan ya biyo bayan rahotanni da ke cewa matsalar tsaron da ta taso a kasar ta lafa, bayan yunkurin juyin mulki da aka yi.

Source: Facebook
Najeriya ta dawo da jirginta daga Benin
Rahoton Zagazola Makama ya ruwaito cewa an yi yunkurin juyin mulki a yau Lahadi 7 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin tsaro sun shaida wa cewa jirgin, wanda aka tura daga Lagos don sintiri da sa ido a yankin, an umarce shi da ya koma sansani bayan samun bayanai.
Bayanan sun nuna cewa an shawo kan lamarin kuma “ba a ga wani barazana ga tsaron kan iyakar Najeriya ba.”
A rahotannin, an ce an murkushe yunkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi wa gwamnatin Shugaba Patrice Talon inda dakarun gwamnati masu biyayya suka kwato cikakken iko.

Source: Facebook
Yadda aka yi yunkurin juyin mulki
Rikicin ya fara ne bayan wasu sojojin da suka yi kaurin suna a cikin kayan soja suka ƙaddamar da farmaki domin hambarar da gwamnati.
An yi ƙoƙarin kutsa wa fadar shugaban kasa da ke Cotonou, amma dakarun gwamnati suka dakile harin.
Bayan haka ’yan tawayen sun mamaye gidan talabijin na gwamnati ORTB, inda suka kwace ikon watsa shirye-shirye.
Rundunar tsaro ta National Guard da sauran sojoji masu biyayya sun kewaye shalkwatar talabijin ɗin, suka killace ’yan tawayen.
Daga bisani, gwamnati ta tabbatar da iko a wuraren gwamnati masu mahimmanci kuma ta kwantar da tarzoma a birnin.
“Matsalar tana ƙarƙashin iko. National Guard ta mamaye komai.”
- In ji wani jami’in tsaro
Rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida, sun nuna cewa ’yan tawayen har yanzu suna cikin gidan talabijin suna tsare, yayin da ake tattaunawa don su mika wuya ba tare da tashin hankali ba.
Babu rahoton tashin hankali ko mace-mace a titunan Cotonou, duk da cewa an bayyana birnin da tashin hankali bayan farkon rikicin.
Ana sa ran gwamnatin Benin za ta fitar da cikakken bayani kan lamarin, ciki har da sunayen ’yan tawayen da yadda yunkurin ya gaza.
An tsare Sylva kan zargin juyin mulki
Mun ba ku labarin cewa sababbin bayanai sun kara bulla a kan yadda aka alakanta tsohon Ministan man fetur, Timipre Sylva da kokarin juyin mulki.
Rahotanni sun ce hukumomin tsaro a kasar nan da suka hada da DIA, tare da EFCC da NFIU ne suka gano kudin da aka so amfani da su.
Kuma bayanai daga sojojin da ke hannun hukumomi sun alakanta tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sylva da yunkurin kifar da gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


