IBB Ya Gano Matsalar Arewa, Ya Fadi Dalilin Rashin Tsaro, Talauci a Yankin

IBB Ya Gano Matsalar Arewa, Ya Fadi Dalilin Rashin Tsaro, Talauci a Yankin

  • Tsohon shugaban kasa, ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana game da rashin tsaro da talauci a Arewa
  • IBB da Janar Alani Akinrinade mai ritaya sun koka cewa Najeriya ta rasa shugabanni masu ɗabi’a, gaskiya da kishin ƙasa
  • Suka ce dabi'u irin na marigayi Janar Hassan Katsina shi ne abin da ya kamata kowa ya yi koyi da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Matsalar tsaro da karuwar talauci a Najeriya sun mamaye tattaunawa a Kaduna yayin da tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya ba da shawara.

IBB da Laftanar Janar Alani Akinrinade mai ritaya sun bayyana damuwa cewa kasar ta rasa shugabanni masu tarbiyya, kishin kasa da nagarta.

IBB ya nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Arewa
Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Gargadin da IBB ya yi ga Arewa

Rahoton Tribune ya ce IBB da tsohon sojan sun bukaci shugabannin su nuna halin kirki irin na marigayi Janar Hassan Usman Katsina.

Kara karanta wannan

An buga rikici da Matawalle a ma'aikatar tsaro kafin Badaru ya ajiye aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana haka ne a taron tunawa da Janar Hassan Katsina karo na biyu da aka gudanar a Kaduna, karkashin cibiyar New Vision Development Initiative (NEVDI).

Dattawan sun gargadi cewa Arewa na ci gaba da shiga matsanancin halin tattalin arziki da zamantakewa saboda halayen shugabanci irin wanda Katsina ya yi ba sa fitowa a cikin ‘yan siyasar yau.

IBB, wanda Kanal Lawal Gwadebe mai ritaya ya wakilta, ya bayyana Hassan Katsina a matsayin “ginshikin cigaban Arewa”, yana mai cewa tawali’unsa, siyasar zaman lafiya da fifita jama’a sun zama abin koyi ga shugabanni.

Ya kara da cewa duk da kasancewarsa jikan sarakuna, Katsina ya kasance mai sauƙin kai da hidima ga al’umma, siffofin da IBB ya ce yanzu sun yi karanci a cikin shugabanni.

“Ya kasance jikan sarakuna amma bai taba daukarsa matsayin gata ba. Har yau, shekaru 30 da rasuwarsa, rashin sa ya bar gibi mai girma.”

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon Sanata a Arewa ya riga mu gidan gaskiya

- Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon shugaban kasa, IBB ya magantu kan rashin tsaron Arewa
Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida. Hoto: Patrick Durand.
Source: Getty Images

Tsohon soja ya yabawa marigayi Hassan Katsina

A nasa bangaren, Akinrinade ya bayyana marigayin a matsayin “yarima a tsakanin sojoji kuma soja a tsakanin yarima”.

Ya tuna rawar da Katsina ya taka a yakin basasa, inda ya fadada rundunar soja kuma ya kare jin dadin sojoji, abin da ya yi karo da korafe-korafen da ake yi yau, cewar Daily Post.

“’Yan kalilan ne ke da gaskiya irin tasa, kishinsa da jajircewarsa wajen kare hadin kan kasa har yanzu suna jan hankalin matasa.”

Sai dai mafi girman gargadin ya fito daga babban bako, Farfesa Abubakar Siddique Mohammed, wanda ya gabatar da rahoto kan halin da Arewa ke ciki tare da alkaluma da suka tayar da hankali a dakin taron.

IBB ya tura sako ga yan Najeriya

A baya, an ji cewa kwanan nan tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya cika shekara 84 a duniya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa gidan malamin addini a Kaduna da dare, sun sace shi

Janar Babangida (mai ritaya) ya bayyana cewa addu'o'in da Musulmai da Kiristoci suke yi, suna da tasiri sosai wajen hadin kan kasar nan.

Tsohon sojan ya bukaci 'yan Najeriya da ka da su gajiya wajen ci gaba da sanya kasar nan cikin addu'a domin samun ci gaban ta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.