"Mun San Dabarunsu" Gwamna Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Garkuwa da Mutane

"Mun San Dabarunsu" Gwamna Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Garkuwa da Mutane

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro musamman ta garkuwa da mutane da ake fama da ita
  • Monday Okpebholo ya nuna cewa akwai hannun 'yan siyasa dumu-dumu kan matsalar garkuwa da mutane domin suna son cimma wani abu kan Shugaba Bola Tinubu
  • Gwamnan ya bayyana cewa sun san dabarun irin wadannan 'yan siyasar kuma ba za su taba bari su yi nasara ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan.

Gwamna Monday Okpebholo ya ce masu garkuwa da mutane na kai hare-hare ne don su yi wa Shugaba Bola Tinubu barazana da tsoratarwa.

Gwamna Okpebholo ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo Hoto: @akpamikoza
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Juma’a lokacin da wata tawaga ta kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ziyarce shi a birnin Benin babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa ya yi karatun ta natsu, ya zakulo abin da ya haddasa rashin tsaro a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Okpebholo ya yi zargi kan rashin tsaro?

Okpebholo ya ce wadanda ke da alhakin sace-sacen mutane a 'yan kwanakin nan suna kokarin tsoratar da shugaban kasa ta hanyar amfani da dabarun tsoratarwa.

“Ba za mu bari barazana ta yi tasiri a kanmu ba. Abin da suke yi yanzu shi ne su je su yi garkuwa da mutane saboda kawai suna so su bata wa shugaban kasa rai."
“Shugaban kasa mai jajircewa ne. Suna yin garkuwa da mutane saboda wani yana son ya yi nasara a zabe, wannan ba daidai ba ne."
"Sun yi wa Goodluck Jonathan haka kuma sun yi nasara, amma yanzu mun san dabarunsu.”

- Gwamna Monday Okpebholo

Okpebholo na kula da mutanen Igbo

Gwamnan ya ce dukkan batutuwan da suka shafi al’ummar Igbo a jihar suna samun kulawa da gaggawa.

Gwamna Okpebholo ya yi zargi kan rashin tsaro
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo Hoto: @akpakomiza
Source: Twitter

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo a Edo, Benjamin Ezewere, ya yaba da abin da gwamnan ya cimma a shekararsa ta farko a mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 sun ajiye banbancin siyasa, sun kafa rundunar yaki 'yan bindiga

Ya kuma yi alkawarin cewa kungiyar za ta ci gaba da goyon bayan gwamnan a kokarinsa na ci gaba da inganta jihar Edo.

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun sace dalibai a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jami'ar jihar Rivers (RSU) da ke Emohua a Rivers.

'Yan bindigan wadanda ake zargin mambobin kungiyar daba ne sun yi awon gaba da dalibai guda biyar bayan sun kutsa kutsa wani gidan haya da dalibai ke zaune a kusa da makarantar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da sace daliban, tana mai bayyana maharan a matsayin kungiyoyin daba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng