'Za Su Sha Jar Miya': Tinubu Ya Ware Wasu Ma'aikata, Ya Ba Su Rancen N3.7bn

'Za Su Sha Jar Miya': Tinubu Ya Ware Wasu Ma'aikata, Ya Ba Su Rancen N3.7bn

  • An tabbatar da raba N3.7bn ga kusan ma’aikata 2,000 a jami’o’i da kwalejoji a kokarin gwamnati na karfafa gwiwar malamai da ma’aikata
  • Gwamnati ta bayyana cewa kaso 17% na masu amfana malamai ne, yayin da 83% suka fito daga bangaren ma’aikatan gudanarwar makarantu
  • An kaddamar da shirin TISSF a 2025 domin ba malamai da ma'aikata damar sayen gidaje, kula da kiwon lafiya, sufuri da kasuwancinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da raba sama da naira biliyan 3.7 a matsayin lamuni ga malamai da ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin fasaha da kuma kwalejojin ilimi a karkashin shirin TISSF.

Daraktar yada labarai ta ma’aikatar ilimin tarayya, Folasade Boriowo, ta bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ta ce kusan mutum 2,000 ne suka amfana a zagayen farko na shirin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An rike 'dan Najeriya da ya rikita Amurka da damfara

Gwamnatin Tinubu ta raba N3.7bn a matsayin bashi ga malamai da ma'aikatan jami'o'i
Shugaba Bola Tinubu a lokacin da zai jagoranci taron FEC a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta ba ma'aikata bashin N3.7bn

A zantawarta da jaridar Punch, Folasade Boriowo ta ce shirin ya shafi jami’o’i, kwalejojin fasaha da kuma kwalejojin ilimi guda 43 a fadin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan ta bayyana cewa an raba kudin ne a tsarin kashi 17 na wadanda suka amfana malamai ne, yayin da sauran kashi 83 suka fito daga ma’aikatan gudanarwa.

Ta kara da cewa akwai gibin jinsi a cikin jerin wadanda suka amfana, inda maza suka kai 83%, mata kuma 17%. A cewarta, gwamnati za ta kara kokari domin karfafa mata su amfana da shirin a zagayen gaba.

Ta jaddada cewa an samar da shirin TISSF ne domin tallafa wa “jajurtattun ma'aikata maza da mata” da ke tabbatar da dorewar tsarin ilimi a kasar nan.

Amfanin lamunin ga malamai da ma'aikata

An kaddamar da shirin a watan Agustan shekarar 2025, tare da ba da damar karbar lamunin har zuwa N10m ba tare da riba ba, wanda bai wuce kaso daya bisa uku na albashin ma'aikaci a shekara ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi magana bayan kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Magaji

Jaridar Tribune ta rahoto cewa malamai da ma'aikata na amfani da kudin wajen gina gidaje, biyan kudin lafiya, sufuri, kananan kasuwanci da bunkasa sana’o’insu.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana TISSF a matsayin ginshikin ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, wanda ma’aikatar ilimi, TETFund da Bankin Masana’antu ke aiwatar da shi.

A cewar ministan, gwamnati ta dauki alkawarin inganta walwala, martaba da arzikin ma’aikatan ilimi don karfafa ingancin cibiyoyin ilimi a nan gaba.

Ministan ilimi, Tunji Alausa ya ce an ba da bashin ne domin inganta rayuwar malamai da ma'aikatan makarantu
Ministan ilimi, Tunji Alausa ya na jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Manufar gwamnati kan ba da bashi kudin

Tunji Alausa ya kara da cewa shirin ya dace da kokarin gwamnati na sauya Najeriya daga tattalin arzikin da ya dogaro da albarkatun kasa zuwa tattalin arzikin ilimi da fasaha.

Baya ga wannan, wata sanarwa daga ma’aikatar ilimi ta ce gwamnati tana ganin TISSF a matsayin wani ginshiki da zai kara farfado da kwarin gwiwa ga malamai.

Hakazalika, shirin zai habaka sha’awar jama'a na yin aiki a bangaren koyarwa, wanda ke fama da karancin ma’aikata, rashin kayan aiki da bincike.

An kafa asusun TISSF a Abuja

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, gwamnti ta kaddamar da asusun TISSF domin bunkasa walwalar ma'aikata da kuma kara masu kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Ministan ya bayyana cewa asusun TISSF na karkashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu da zummar daga darajar bangaren ilimi.

A cewar ministan, ma'aikatar ilimi ta tarayya da kuma asusun TETFund ne suka samar da shirin tallafin tare da hadin gwiwar Bankin Masana'antu (BoI).

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com