Tinubu, Ministansa da Gwamna Sun Shiga Matsala, Za Su Kare Kansu a Kotu
- Kamfanin Winhomes Estate ya shigar da ƙarar gaggawa a kotu domin dakile gwamnatin tarayya da na Lagos
- An bukaci kotun ta hana gwamnati shiga ko rusa filinsa hekta 18 a Okun-Ajah da ke jihar Lagos
- Masu ƙarar sun zargi Ma’aikatar Ayyuka, Gwamnatin Lagos da Hitech da mamaye fili da karfi ba tare da sanarwar kwacewa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - Babbar rigimar shari’a na tasowa a Lagos yayin da kamfanin Winhomes Estate ya shigar da gwamnati kara kotu.
Kamfanin ya shigar da ƙarar a domin hana Gwamnatin Tarayya, Ministan Ayyuka David Umahi masa katsalandan.

Source: Facebook
Musabbabin maka Tinubu, gwamna a Lagos
Rahoton Leadership ya ce sauran wadanda ake kara akwai Gwamnatin Lagos da kamfanin Hitech domin hana su shiga ko rusa wani fili.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu ƙarar, waɗanda ke wakiltar kansu da daruruwan mutanen da suka sayi filayen Winhomes Estate, suna roƙon kotu ta hana waɗanda ake ƙara shiga ko rushe gine-ginen filin su mai hektar 18.838.
Winhomes na zargin gwamnati da Hitech da “rusa gine-gine, dasa allunan sanarwa, girka hasken fitilu da yin alamomi” a filin da nufin haɗa shi da aikin Lagos–Calabar da kuma tashar jirgin ƙasa da ake shirin ginawa.
Masu ƙarar sun ce filin na da sahihin takardun mallaka, sannan gwamnati ta tabbatar cewa filin ba ya cikin layin hanyar gabar teku.
Duk da haka, an nuna cewa sojoji, jami’an Ma’aikatar Ayyuka da ma’aikatan Hitech sun “kutsa kai da karfi” suka fara rushe-rushe da ayyukan gini a filin.
Masu ƙarar sun jaddada cewa babu gwamnati ko ta jihar ko ta tarayya da ta aiko musu da sanarwar kwace fili kamar yadda dokar mallakar fili ta tanada.

Source: Getty Images
Zargin da ake yi wa gwamnatin Lagos
Takardar ta ci gaba da cewa an yi wannan mamaya ne tare da sojoji, jami’an Task Force na Ofishin Gwamnan Lagos, Sanwo-Olu da kuma ma’aikatan Hitech.
Masu ƙarar suna cewa idan kotu ba ta shiga tsakani kai tsaye ba, wannan aiki zai raba su da filin gaba ɗaya, kuma lalacewar da za ta faru ba za ta iya warkewa ta hanyar kudin diyya kawai ba.
Haka kuma sun shigar da takardar gaggawa wadda ke cewa an riga an kafa allunan sanarwa, fitilun halogen da janareto a filin, kuma ana tsare da ‘yan sanda masu makamai.
Kamar yadda dokoki a Lagos suka tanada, masu ƙarar sun riga sun aika da dukkan waɗanda ake ƙarawa, ciki har da lauyan gwamnatin tarayya, domin su nuna an shirya shigar da cikakkiyar ƙara.
Kwastam: An shigar da Tinubu kara kotu
Kun ji cewa wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Dr Bolaji Akinyemi, ya shigar da kara a kotu yana kalubalantar shugaban Najeriya, Bola Tinubu.
Dr. Akinyemi ya shigar da karar ne yana kalubalantar sahihancin tsawaita wa’adin shugaban kwastam, Bashir Adeniyi da wa'adinsa ya kare.
Mai karar na neman kotu ta hana ci gaba da wa’adin Adeniyi da kuma yanke hukunci cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


