Muhuyi Magaji Ya Ambaci Ganduje da Wani Mutum 1 bayan Fitowa daga Hannun 'Yan Sanda

Muhuyi Magaji Ya Ambaci Ganduje da Wani Mutum 1 bayan Fitowa daga Hannun 'Yan Sanda

  • Rundunar 'yan sanda ta bada belin tsohon shugaban hukumar PCACC ta Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado kwana guda bayan kama shi
  • Muhuyi Rimin Gado ya bayyana cewa an sako shi a ranar Asabar amma zai sake komawa Abuja ranar Litinin mai zuwa domin cika sharuddan beli
  • Gwamnatin jihar Kano dai ta nuna damuwa kan yanayin da aka kama Muhuyi Magaji a ranar Juma'a, tana mai cewa hakan ya saba wa dokar Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rundunar 'yan sanda ta sako tsohon shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Muhuyi Magaji Rimin Gado ya shaki iskar 'yanci kasa da sa'o'i 24 bayan dakarun 'yan sanda daga Abuja, sun masa dirar mikiya a ofishinsa da ke titin Zaria a cikin garin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi magana bayan kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Magaji

Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Tsohon shugaban hukuma PCACC, Barista Muhuyi Magaji Rimingado Hoto: Muhuyi Magaji
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa 'yan sanda sun kama Muhuyi a ofishinsa, kana suka tafi da shi zuwa hedkwatar 'yan sanda da ke Bompai kafin a wuce da shi Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta yi Allah wadai da kama Rimin Gado, tana mai bayyana cewa hakan ya saba wa umarnin kotu wacce ta hana kama shi ko cin zarafinsa.

Ta kuma yi kira ga hukumomin gwamnatin tarayya da su bi doka da 'yan cin dan kasa a wajen tafiyar da lamarin Barista Muhuyi.

Kwana daya bayan kama shi, rundunar 'yan zanda ta saki tsohon shugaban PCACC a yau Asabar, 6 ga watan Disamba, 2025.

Muhuyi Magaji Rimin Gado ya fadi dalilin kama shi

Yayin da yake magana a ranar Asabar bayan fitowarsa daga hannun 'yan sanda, Muhuyi Rimin Gado ya ce an sako shi ne a kan beli kuma zai koma Abuja a ranar Litinin domin kammala cika sharuddan belinsa.

Kara karanta wannan

To fa: An kama tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji

Lauyan ya bayyana cewa 'yan sanda sun kama shi ne bayan sun samu korafe-korafe guda biyu da aka shigar a kansa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wane korafi Ganduje ya kai kan Muhuyi?

Ya ce wadanda suka kai korafe-korafen sune tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Bala Inuwa, tsohon shugaban kamfanin noma na Kano, KASCO.

An ruwaito cewa shari’o’in da suka hada da maganar badakalar Dala Inland Dry Port da ta shafi Ganduje da kuma rikicin KASCO duk suna nan a gaban kotu, kuma ba a kai ga yanke hukunci ba.

Gaduje da Muhuyi Magaji.
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje CFR, Muhuyi Magaji
Source: Facebook

Martanin gwamnatin Kano kan kama Muhuyi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan yadda aka tura dakarun 'yan sanda dauke da makamai suka tafi da Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar Kano, Barista Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ya ce gwamnati ta yi Allah wadai da karfa-karfar da aka nuna wajen kama Rimin Gado.

Ya kara da cewa akwai umarnin kotun jihar Kano da ya hana ‘yan sanda kama ko razana Rimin Gado, amma duk da haka aka take wannan umarni.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262