Liman da Masallata Sun Rasa Ransu bayan Harin ’Yan Bindiga ana Sallar Asuba
- Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan hari kan masallata a jihar Sokoto ana tsaka da sallah
- An ce maharan sun kai harin ne a lokacin sallar asuba inda suka kashe mutane biyu ciki har da limamin masallaci
- Har ila yau, yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu masu ibada, abin da ya ƙara nuna yadda rashin tsaro ke taɓarɓarewa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Mazauna wani yanki a jihar Sokoto sun shiga mummunan yanayi bayan harin yan bindiga a masallaci.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun farmaki masallatan ne yayin sallar asuba a yau Asabar 6 ga watan Disambar 2025.

Source: Original
Rahoton Bakatsina da ke kawo bayanai kan lamarin tsaro shi ya tabbatar da haka a yau Asabar a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga suka addabi masallatai
Wannan ba shi ne karon farko ba da yan bindiga ke kai hari a masallaci a jihar Sokoto wanda yake jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Jama'a sun dimauce a lokacin da wasu ‘yan bindiga sun kai hari a masallaci a ƙauyen Marnona, da ke jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun dura a masallacin da Asuba, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Ana zargi maharan sun fito daga sansanonin ‘yan bindiga a dazuzzukan Sokoto da Zamfara domin kawo harin.

Source: Facebook
Harin da yan bindiga suka kai masallaci
An ce an kai harin ne da sassafe yau lokacin sallar asuba inda ‘yan bindiga suka afka wa masu ibada.
Lamarin ya faru ne a yankin Kiba Ruwa da ke ƙaramar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane biyu, ciki har da limamin da yake jagorantar sallar a lokacin harin.
Haka kuma, maharan sun yi garkuwa da wasu daga cikin masu ibadar, abin da ya ƙara tayar da hankula game da tsanantar matsalar tsaro a yankin Arewa.
Mazauna yankin sun fusata kan hare-haren
Wasu mazauna yankin na korafi kan hare-hare wanda ya sake haifar da tambayoyi game da hare-haren ta'addanci wanda ke kara kamari.
Yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masallatai da coci da kuma makarantu da yara ke zuwa, ana tambayar ta ina talawaka za su saka kansu.
Yankin Arewacin Najeriya na ci gaba da fama da matsalolin tsaro wanda ya ke shafar Musulmi da Kirista yayin wasu ko ke zargin ana hallaka Kiristoci da wata manufa.
'Yan bindiga sun kai hari a masallacin Juma'a
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun kai hari masallaci ana tsakiyar sallar asuba a kauyen Yandoto da ke yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Rahotanni daga mutanen kauyen sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe akalla mutane biyar a masallacin, sun raunata wasu da dama.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya ce har lokacin bai samu rahoton harin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

