Sanata Ndume Na Neman Dawo da Hannun Agogo Baya game da Jakadun da Tinubu Ya Nada

Sanata Ndume Na Neman Dawo da Hannun Agogo Baya game da Jakadun da Tinubu Ya Nada

  • Sanata Ali Ndume ya soki jerin sababbin jakadun Najeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Majalisar Dattawa domin tantancewa
  • Ndume ya bayyana cewa ba a bi tanadin kundin tsarin mulki ba wajen raba mukaman jakadun tsakanin jihohi 36 da ake da su a Najeriya
  • Kwararren 'dan majalisar ya shawarci shugaban kasa ya janye jakadun da ya tura majalisa, kana ya sake nazari domin yi wa kowane yanki adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya nemi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ua janye jakadun da ya nada.

Ndume ya bukaci Tinubu ya janye jerin sunayen jakadu da ya tura majalisar dattawa saboda “ba su mutunta tsarin dokar dabi'a,” da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Sanata Ali Ndume.
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume Hoto: Sen. Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Alhamis da ta gabata, Majalisar dattawa ta karɓi jerin sunayen jakadun kuma ta mika wa kwamitin harkokin ƙasashen waje don tantancewa.

Korafin Ali Ndume kan sababbin jakadu

A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Sanata Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce rabon da aka yi tsakanin jihohi ya nuna ba a yi adalci ba.

Ya ce wasu jihohi sun samu har guda uku ko huɗu, wasu kuwa ba su samu ko mutum ɗaya ba, ciki har da Jihar Gombe.

Ndume ya ce yayin da jihar Yobe ta rasa mutum daya da aka dauka bayan rasuwar Sanata Adamu Garba Talba, gaba ɗaya Arewa maso Gabas ta samu mutum bakwai kacal a cikin jakadun.

Ndume ya bukaci Tinubu ya janye jakadun

Sanatan ya gargadi Shugaba Tinubu da kauce wa duk wani mataki da ka iya haifar da tashin hankali na kabilanci, rashin yarda da gwamnati, ko kuma rashin daidaito a rabon mukaman ƙasa.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya

Ya ce:

“A wannan lokaci mai muhimmanci, ba daidai ba ne a aikata abin da zai janyo kiyayya tsakanin jihohi. Ina kira ga Shugaba Tinubu da ya janye jerin jakadun, a turo sabo wanda ya dace da tanadin kundin tsarin mulki.”

Ndume ya ce yana da tabbacin Shugaba Tinubu “mutum ne mai hangen nesa ne kuma shugaba mai son haɗa kan kowa da kowa a kasar nan."

Shawarar Sanata Ndume ga Shugaba Tinubu

Don haka, sanatan ya ci gaba da cewa ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa kowace jiha na da wakilci kuma kowace jiha da kowane yanki sun samu adalci,

Bugu da kari, Ndume ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta nuna cewa tana bin tsarin raba mukaman tarayya cikin gaskiya, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Ya kammala da cewa yin haka ne zai kara haɗin kan ƙasa, amincewar jama’a ga gwamnati, da kuma kwantar da hankalin ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro

Shugaba Tinubu da Ali Ndume.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Sanata Ali Ndume Hoto: @OfficialABAT, Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Jerin sababbin jakadun Najeriya

A baya, mun kawo muku cikakken jerin sababbin jakadun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatar da nadinsu.

Bayanai sun nuna cewa wadanda aka nada sun kunshi cikakkun jakadu masu gogewa a harkokin jakadanci da kuma sababbin shiga.

Daga cikin jakadun akwai Ibok-Ete Ekwe Ibas (rtd), tsohon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa kuma tsohon shugaban rikon Ribas da tsohon hafsan sojin kasa kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262