Yadda Yerima Ya Yi Aure da Abubuwan da Suka Faru bayan Rigima da Wike

Yadda Yerima Ya Yi Aure da Abubuwan da Suka Faru bayan Rigima da Wike

  • Ana ta yada bayanai mabamabanta kan Laftanan Adam Muhammad Yerima bayan rigima da Nyesom Wike
  • An ce Yreima ya yi auren sirri da masoyiyarsa a Kaduna makonni da ce-ce-ku-ce game da takaddamar da ta faru
  • Hotuna da bidiyon bikin su sun sake jawo martani a kafafen sada zumunta, yayin da iyalan amarya suka yi masa addu’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - An tabbatar da cewa Laftanan Adam Muhammad Yerima ya yi aure a asirce a jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan rigimarsa da Nyesom Wike da kuma ce-ce-ku-cen da ya biyo baya wanda ya ja hankulan mutane.

Yerima ya yi auren sirri a Kaduna bayan rigima a Kaduna
Lt. Adan Yerima lokacin aurensa da rigimar da ya yi da Wike. Hoto: @mc-raheena.
Source: Instagram

Rahoton Daily Trust ya ce Yerima ya yi auren ne cikin sirri domin kiyaye ka'idojin aikinsa da kuma gudun yada lamarin a kafofin sadarwa.

Kara karanta wannan

Tijjani Gandu ya fadi gaskiyar alakar da ke tsakaninsa da jaruma Maryam Booth

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jawo shaharar Laftana Yerima

Sunan jami'in sojan ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta saboda takaddamarsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Yerima ya fara shahara ne bayan bullar bidiyon da ya hana tawagar ministan shiga wani gida da aka danganta da tsohon hafsan sojojin ruwa.

Wannan rikicin ya jawo muhawara sosai har ya haifar da yaduwar hotuna da bidiyon bogi da aka kirkira da AI, suna nuna shi cikin yanayi daban-daban marasa tushe.

Cikin lokaci kadan, Yerima ya zama tauraro a intanet, hotuna da yawa sun bayyana suna nuna shi yana yi wa mata daban-daban tayin aure.

An wallafa hotunan auren Yerima a Kaduna
Laftanan Yerima da surkansa lokacin aurensa a Kaduna. Hoto: @mc-raheena.
Source: Instagram

Yadda Yerima ya yi aure a Kaduna

Duk da wannan hayaniya, an fitar sababbin hotuna da suka bayyana aurensa da Khadija wanda aka tabbatar aure ne na gaskiya.

Iyalan amarya sun ce an yi bikin ne cikin sirri a Kaduna, tare da yan uwansu tsiraru kawai.

Kara karanta wannan

Bidiyon da ya sa wasu 'yan Najeriya ke neman sai Matawalle ya yi murabus

An bayyana cewa amaryar ‘yar asalin jihar Zamfara ce, ana kiran inkiyar gidansu da "Anka", duk da cewa ba a tabbatar da cikakken sunanta ba.

Shahararriyar mai nishadantarwa ta Arewa, MC Raheema, ita ce ta fara wallafa hotunan a Instagram tare da sakon:

“Allahumma Barik, abokiyata Khadijah ta yi aure da saurayinta, Laftanan A.M Yerima. ina taya ma'auratan murna, Allah ya ba su zaman lafiya.”

Rubutun ya dauki hankalin jama’a cikin mintuna kaɗan, inda dubban mutane suka yi martani da sake yada shi.

Wasu sun fara zargin hotunan bogi ne har sai da wasu bidiyo na gaskiya suka fara bayyana.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga Yerima da matarsa a gidan iyayenta, yayin da wani dattijo daga dangin amarya ke yi musu nasiha da addu’a.

Tijjani Gandu ya magantu kan Maryam Booth

A wani labarin, an yi ta maganganu a kafofin sadarwa na zamani bayan yada jita-jitar auren Tijjani Gandu da Maryam Booth.

Gandu ya fadi alakar da ke tsakaninsa da jarumar inda ya ce shi da Maryam sun dauki wasu hotuna ne na wata waka.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yabi sulhu da 'yan bindiga, ya fadi amfanin da aka samu a Katsina

Sai dai hadimin na gwamnan jihar Kano ya ce yada hotunan a yanar gizo ya jawo rudani har lamarin ya so ya wuce gona da iri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.