Ministan Tinubu Ya 'Wawure' Naira biliyan 16.5 na Gyaran Gadar Arewa? Gaskiya Ta Fito

Ministan Tinubu Ya 'Wawure' Naira biliyan 16.5 na Gyaran Gadar Arewa? Gaskiya Ta Fito

  • Karamin Ministan Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari ya musanta zargin cinye kudin gyaran gadar Namnai da ke karamar hukumar Gossol a Taraba
  • Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Abdulmumuni Imam ne ya zargi Ministan da karkatar da kudin gyaran gadar wanda ya kai Naira biliyan 16.5
  • Lauyan ministan ya ce tuni suka fara bin matakan shari'a domin hukunta wanda ya kirkiro wannan karya saboda ya gagara gabatar da hujjoji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba, Nigeria - A yan kwanakin nan ne aka fara yada jita-jita musamman a kafafen sada zumunta cewa karamin Ministan Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari ya cinye kudin gyaran gadar Namnai.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

Jita-jitar ta yi ikirarin cewa Ministan ya karkatar da Naira biliyan 16.5 da aka ware domin sake gina gadar Namnai da ta karye a ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba.

Uba Maigari.
Karamin Ministan Ci Gaban Yankun, Uba Maigari Hoto: @HMSRegionalDev
Source: Facebook

Ministan Tinubu ya karkatar da N16.5bn?

Amma karamin Ministan ya fito ya yi watsi da wannan zarge-zargen, yana mai cewa babu kanshin gaskiya a ciki, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Yayin da yake magana da manema labarai a Jalingo ta bakin babban lauyansa, Ibrahim Effiong, ministan ya bayyana cewa wannan zargi “shirme ne kawai da aka kirkira domin rudar jama’a.”

Ya ce tuni ministan ya gurfanar da wanda ya yi zargin, wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Abdulmumuni Imam, a kotu.

Ya kara da cewa duk da girman wannan zargi da Imam ya yi, ya kasa gabatar da kowanne irin shaida a gaban kotu, maimakon haka ma ya gudu ya buya, in ji Daily Post.

Wane mataki Uba Maigari ya dauka?

A cewar Effiong, zargin cin amana ba tare da wata hujja ba babban laifi ne bisa dokar laifuffukan yanar gizo saboda haka ana bin matakin shari’a domin ya zama izina ga masu yada kalaman karya a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukumar da ke fama da rashin tsaro ya raba motoci ga kansiloli

A baya, Imam ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi har Naira biliyan 16.5 domin gyara gadar wacce ta rushe amma wai ministan ya karkatar da kudin.

Uba Maigari.
Karaminin Ministan Ci Gaban Yankuna a Najeriya, Uba Maigari Hoto: @HMSRegionalDev
Source: Twitter

Mutumin ya kuma yi zargin cewa ministan ya nemi jami’an tsaro su kama shi saboda yana sukar halin da gadar ke ciki da yadda aka yi sama da fadi da kudin gyaranta.

Sai dai lauyin ministan ya ce babu wata shaida da ta nuna an karkatar da ko sisi, kuma duk ikirarin Imam “ƙirƙirarrar karya ce mara tushe.

Ministan Abuja ya kori shugaban FCT-IRS

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Harkokin Babban Birnin Tarayya Abuja , Nyesom Ezenwo Wike ya ya tsige shugaban hukumar tattara harajin Abuja, Michael Ango, nan take.

Wike ya umarci jami’i mafi girma a FCT-IRS da ya gaggauta karɓar jagoranci domin ci gaba da gudanar da ayyukan wannan muhimmiyar hukumar ta tattara kudaden shiga a Abuja.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin Wike na daukar matakin ba, lamarin da ya sa aka fara tantama da tambayoyi kan dalilin tsige Mista Ango daga kan mukaminsa cikin gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262