Gwamna Inuwa Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Zakulo Abin da Ya Haddasa Rashin Tsaro a Arewa
- Yankin Arewacin Najeriya na ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro wadda ta jawo asarar rayuka da rasa dukiya mai tarin yawa
- Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya yi tsokaci kan matsalolin da suka rura wutar rikicin
- Gwamna Inuwa ya kuma bayyana kokarin da suke yi domin ganin an shawo kan matsalar wadda aka dade ana fama da ita
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a yankin.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ce rashin fahimtar korafe-korafen da suka tura ‘yan bindiga su ɗauki makami na ɗaya daga manyan dalilan da suka ta’azzara matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Gwamna Radda ya yabi sulhu da 'yan bindiga, ya fadi amfanin da aka samu a Katsina

Source: Facebook
Gwamna Inuwa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Arewa sun kafa hukuma
Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnonin jihohin arewa 19 sun amince da kafa wata hukumar hadin-gwiwar tsaro ta yankin Arewa.
Gwamnan ya ce kowace jiha za ta rika ba da Naira biliyan 1 a duk wata domin fuskantar matsalolin yin garkuwa da mutane, ‘yan bindiga, da rufe makarantu.
An cimma wannan matsaya ne a lokacin taron gwamnonin Arewa a farkon makon nan, bayan karuwar hare-hare da suka haddasa garkuwa da mutane da dama da kuma rufe makarantu a jihohi da dama.
Me Gwamna Inuwa ya ce kan rashin tsaro?
Gwamnan ya kara da cewa wani babban ɓangare na tabarbarewar tsaro ya samo asali ne daga rashin adalci da wariyar da ake nuna wa al’ummar makiyaya.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya
Ya ce hakan ya haifar da ɓacin rai, takaici, da yanayi wanda miyagun kungiyoyi suka yi amfani da su.
"Daga cikin dalilan da suka sa aka rabu yanzu ake shiga daji mutane ne da suka san daji. akasari kiwo suke yi a daji amma saboda rashin bin doka ya sa babu burtali babu labi babu gandun daji babu gandun kiwo a wuraren da suka saba."
''Kuma za ka ga har gefen hanya mutane sun yi shuka to ka ga a garin suna kiwo sun zo sun yi ta'adi suka rasa dukiyoyinsu."
- Gwamna Inuwa Yahaya
Ya bayyana cewa suna fuskantar zalunci daga jami'an tsaro, hukumomin shari'a ko mutanen gwamnati.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
Sai dai, ya bayyana cewa duk da abubuwan da aka yi musu, bai kamata su dauki doka a hannunsu ba.

Source: Facebook
Gwamna Inuwa ya ba da shawara
Gwamna Inuwa ya jaddada cewa magance tushen matsalolin ciki har da wariya, rashin adalci da matsin tattalin arziki shi ne ginshiƙin kawo ƙarshen rikicin.
Gwamna Yahaya ya ce sabon tsarin tsaron na yankin zai inganta musayar bayanan sirri, hadin-kai a ayyukan tsaro, da dabarun rigakafi a dukkan jihohin da matsalar ta shafa.
Gwamna ya yabi sulhu da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yaba kan zaman lafiyar da aka samu sakamakon sulhu da 'yan bindiga.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa sulhun da aka yi ya jawo mutane sun samu kwanciyar hankali a yankunan da ke fama da rashin tsaro.
Hakazalika, ya nuna cewa yanzu ya rage samun rahotannin kai hari daga hukumomin tsaro, sabanin yadda yake samu a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
